Fadar shugaban kasa ta nisanta kanta daga wasu shafukan zumunta da aka bude da sunan Yusuf Buhari

Fadar shugaban kasa ta nisanta kanta daga wasu shafukan zumunta da aka bude da sunan Yusuf Buhari

- Fadar shugaban kasa ta yi watsi da wasu shafukan zaumunta da aka bude da sunan Yusuf Buhari

- Ta ce Yusuf baya kowani dandalin zumunta

- Femi Adesina ya gargadi masu suyi masa sojan gona da su bari

Fadar shugaban kasa a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba ta nisanta kanta daga wasu shafukan zumunta da aka bude da suna dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf.

Mai ba Shugaban kasa shawara akan kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina ya bayyana cewa Yusuf baya kowani dandalin sada zumunta.

Fadar shugaban kasa ta nisanta kanta daga wasu shafukan zumunta da aka bude da sunan Yusuf Buhari

Fadar shugaban kasa ta nisanta kanta daga wasu shafukan zumunta da aka bude da sunan Yusuf Buhari
Source: Depositphotos

Adesina ya bayyana cewa shafukan zumunta sun hada da wani shafin Instagram da aka bude kwanan nan wadda ya samu dubban mabiya, ana amfani da wajen bayyana ra’ayin Yusuf ba tare da sanin shi ba.

KU KARANTA KUMA: Muna maraba da matakin PDP – Kwankwasiyya

Don haka ya shawarci jama’a da suyi watsi da irin wadannan shafukan sannan ya gargadi masu gudanar da irin wadannan shafukan da suna Yusuf da sauran ahlin shugaban kasar da su daina yi musu sojan gona.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Jam’iyyar a tsarin gudanarwan tat ace za’a samar dad an takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct”kenan a turance.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel