Rashin tabbass a Kano yayinda tsohon gwamna Shekarau ya dakatar da sauya shekarsa zuwa APC

Rashin tabbass a Kano yayinda tsohon gwamna Shekarau ya dakatar da sauya shekarsa zuwa APC

- Zargin cewa Shekarau na shirin komawa APC ya haifar da rudani a jihar Kano

- Akwai rade-radin cewa sauya shekar Shekarau zai karawa Shugaba Muhammadu Buhari karfi a jihar

Akwai rade-radin cewa shirin da Ibrahim Shekarau ke kullawa na sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya haifar da rashin tabbass ga wasu yan siyasa dake sa ran gammayar Shekarau da Rabiu Kwankwaso zai kawar da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Shekarau na iya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na iya tabbatar da tazarcen Gwamna Abdullahi Ganduje wadda Kwankwaso ya sha alwashin dakatar da tazarcensa.

Rashin tabbass a Kano yayinda tsohon gwamna Shekarau ya dakatar da sauya shekarsa zuwa APC

Rashin tabbass a Kano yayinda tsohon gwamna Shekarau ya dakatar da sauya shekarsa zuwa APC
Source: Depositphotos

Wani hadimin tsohon gwamnan ya sanar da sauya shekarsa daga PDP zuwa APC sai dai kuma abun ya zo da rudani lokacin da Shekarau ya karyatan cewa akwai wani abu makamancin haka na shirin sauya sheka.

KU KARANTA KUMA: APC ta rage farashin fam din takara, tayi alkawarin fitar da dan takaran shugaban kasa a ranar Alhamis

A halin da ake ciki, Malam Ibrahim Shekarau a wani jawabi da mu ka samu daga Magoya bayan sa, ya tabbatar da cewa babu gaskiya a cikin jita-jitar da ake yadawa cewa ya bar PDP.

Tsohon Gwamnan yace kawo yanzu yana nan a babbar Jam’iyyar adawar kasar.

Ibrahim Shekarau wanda yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP yace ba su yi na’am da rusa shugabancin PDP da aka yi a Kano ba kuma tuni su ka maka uwar Jam’iyya kara a gaban wani Kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel