2019: Wasu matsaloli 2 sun fara sukurkuta jam’iyyar APC

2019: Wasu matsaloli 2 sun fara sukurkuta jam’iyyar APC

- Takaddama a kan hanyar da za a yi amfani da ita wajen fitar da ‘yan takarar da zasu fafata a zaben 2019 karkashin APC na cigaba da jan hankalin ‘ya’yan jam’iyyar

- Ana cigaba da mahawara a kan batun bawa ‘yan jam’iyya damar zaben ‘yan takara ko kuma amfani da wakilai (daliget)

- Wata sabuwar matsala da ta sake saka ‘ya’yan jam’iyyar ta APC cikin damuwa ita ce ta tsadar kudin fom din takara

A yayin da batun hanyar da za a bi wajen fitar da ‘yan takara a APC ke cigaba da jan hankali da jawo cece-kuce, sai ga shi shugabancin jam’iyyar ya kara jawo magana bayan bayyana cewar za a sayar da fam din takarar shugaban kasa a kan miliyan N55m.

Karin kudin fam din kujeru a APC ya saka masu son yin takarar gwamnoni da majalisa a jam’iyyar guna-guni tare da kira ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) da ya sake duba batun farashin fam din.

2019: Wasu matsaloli 2 sun fara sukurkuta jam’iyyar APC

Tinubu, Oshiomhole, Osinbajo da Buhari a wurin taron APC
Source: Depositphotos

Tuni wasu mambobin APC suka ja layi tsakaninsu da kwamitin gudanarwa a kan tashin gwauron zabin da farashin fam din ya yi a wannan karon.

Wasu dake burin yin takara a APC sun aike da takardar korafi ga NWC a kan su rage farashin fam din da kuma kudin na-gani-ina-so da suka fitar tare da yin barazanar zasu shigar da karar jam’iyyar muddin ba ta gaggauta rage kudin fam din ba.

DUBA WANNAN: Uwar jam'iyyar PDP ta sake rushe kwamitin rikon jam'iyyar a jihar Kano

Hatta shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi korafi da tsadar kudin fam din takarar shugaban kasa.

APC ta ce masu son takarar gwamna zasu yanki fam a kan miliyan N22.5, masu takarar sanata zasu sayi nasu a kan miliyan N8.5m, majalisar wakilai a kan miliyan N3.8m, yayin da masu takarar majalisar dokokin jihohi zasu yanki nasu fam din a kan miliyan N1.1m.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel