China ta tsare musulmi yan Uighurs miliyan daya

China ta tsare musulmi yan Uighurs miliyan daya

- Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a saki Musulmai yan kabilar Uighurs dake tsare

- Hakan ya biyon bayan rahoton da ta samu cewa an tsare musulmai miliyan guda

- An tsare su ne da sunan yaki da ta’addanci

Rahotanni sun kawo cewa Majalisar Dinkin Duniya tace tana da labarin dubban musulmai yan kabilar Uighurs da aka kama a kasar China.

Don haka majalisar duniyan ta bukaci a saki mutanen wadanda aka tsare da sunan yaki da ta’addanci, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

China ta tsare musulmi yan Uighurs miliyan daya

China ta tsare musulmi yan Uighurs miliyan daya
Source: Depositphotos

Matakin na zuwa ne bayan wani kwamitin majalisar ya bada rahoton cewa ana tsare da musulmi 'yan kabilara ta Uighurs sama da miliyan daya a wasu sansanoni da sunan sauya musu halayya a garin Xinjiang da ke yammacin kasar.

Yan kabilar ta Uighurs su ne 40% na mazauna yankin. Sai dai hukumomin China sun musanta rade-radin.

KU KARANTA KUMA: Bamu tsayar da kowani dan takaran shugaban kasa ba – Afenifere sun maida martani ga rahoton tsayar da Buhari

A wani lamari na daban, fitaccen Sanatan Jam’iyyar APC mai mulki Kwmared Shehu Sani yayi bayani a shafin sa na sadarwa na Tuwita inda ya nemi mutanen Yankin Afrika su cigaba da alaka da Kasar Sin watau China.

Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya nemi Afrika ta karfafa alakar ta da China musamman a bangaren tattalin arziki.

A cewar Sanatan, Kasar ta China babbar kawa ce ta Afrika. Sai dai kuma Sanatan ya nemi Najeriya ta bi a hankali da kasar. Kwamared Shehu Sani ya nemi Najeriya da ma Afrika su guji maida kan su wuraren da Kasar China za ta rika kawo kaya marasa inganci su na jibgewa.

Bayan nan kuma dai Sanatan ya nemi Najeriya ta bi a hankali da tsarin bashin China.

Har wa yau babban ‘Dan Majalisar na Jihar Kaduna ya bayyana cewa akwai bukatar China ta kara dagewa wajen ganin an daina nunawa bakaken fata na Afrika wariyar launin fata. Ana kukan cewa ana tsangwamar bakaken mutane a Kasar Sin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel