Majalisar dokoki a Ogun ta yi watsi da bukatar sauya shekar wasu yan majalisu zuwa PDP

Majalisar dokoki a Ogun ta yi watsi da bukatar sauya shekar wasu yan majalisu zuwa PDP

- Majalisar dokoki ta jihar Ogun ta yi watsi da kudirin wasu mambobinta biyu na sauya shekadaga APC zuwa PDP

- Majalisar ta yanke wannan hukunci ne bayan da yan majalisun biyu suka gaza kawo hujjar cewa akwai rikici da rabuwar kai a APC

- A bangare daya kuwa, kakakin majalisar ya karanta wasikar wani mamba na sauya sheka daga PDP zuwa APC

Rikici ya barke a cikin majalisar dokoki ta jihar Ogun a ranar Talata, bayan da majalisar ta yi watsi da shirin wasu mambobinta guda biyu na sauya sheka daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Rahotanni sun bayyana cewa yan majalisun biyu sun gaza tabbatar da cewa akawai rabuwar kai a cikin jam'iyyar APC kamar yadda suka bayyana a matsayin dalilinsu na sauya shekar.

Mambobin da suka dau kudirin sauya shekar, mamba mai wakiltar mazabar Remo ta Arewa, Mr. Biyi Adeleye da kuma takwaransa daga mazabar Ogun ta hayin rafi, Mr. Harrison Afeyemi, wadanda suka bayyanawa majalisar kudirinsu na sauya shekar a cikin wasiku mabanbanta, da kakakin majalisar, Mr. Suraj Adekunbi ya karanta.

KARANTA WANNAN: A cikin shekaru 2 zan farfado da tattalin arzikin Nigeria idan aka zabe ni a 2019 - David Mark

Majalisar dokoki a Ogun ta yi watsi da bukatar sauya shekar wasu yan majalisu zuwa PDP

Majalisar dokoki a Ogun ta yi watsi da bukatar sauya shekar wasu yan majalisu zuwa PDP
Source: Facebook

A wasikar da ya aikawa majalisar, Mr. Adeleye ya bayyana cewa akwai rabuwar kawuna da kuma rikicin cikin gida a jam'iyyar ta APC a jihar da kuma matakin kasa, wanda hakan ne ya tilastashi bayyana kudirinsa na barin jam'iyyar.

Sai dai, shugaban masu rinjaye na majalisar, Mr. Yinka Mafe, a lokacin da ya ke maida jawabi bayan da kakakin majalisar ya karanta wasikar, ya bukaci majalisar da ta yi watsi da wadannan dalilai da yan majalisar suka bayar.

Mafe ya tabbatar da cewa babu rabuwar kawuna a cikin jam'iyyar ta APC.

"Zai zama babban kuskure idan har muka kyale wannan maganar ta tafi hakanan, domin sam babu rabuwar kai ko rikicin cikin gida a cikin jam'iyyar mu"

"Ina roko majalisa ta umurce shi da ya zo ya kawo hujjoji na cewar akwai rabuwar kawuna a APC. idan kuwa ya kasa, to ya kamata kakakin majalisar ya yi amfani da kujerarsa wajen daukar matakin da ya dace," a cewar shugaban masu rinjaye.

KARANTA WANNAN: A cikin shekaru 2 zan farfado da tattalin arzikin Nigeria idan aka zabe ni a 2019 - David Mark

Kakakin majalisar shima ya amince da cewa "babu wani rikicin cikin gida ko rabuwar kawuna a APC, daga matakin jiha har zuwa na kasa"

"A dai dai wannan lokaci, zamu yi watsi da wannan kudiri na yan majalisar, har sai lokacin da suka kawo hujjoji na cewar akwai rikici da rabuwar kai a cikin jam'iyyar" a cewar Adekunbi.

Haka zalika a ranar Talata a zaman da majalisar ta yi, kakakin majalisar ya karanta wata wasika daga mambanta, Mr. Bowale Sollaja (dan majalisa mai wakiltar mazabar Ijebu ta Arewa), wanda ya bayyana kudirinsa na barin jam'iyyar PDP zuwa APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel