Wani Matashi ya ƙulla tuggun garkuwa da kisan Mahaifin sa a jihar Osun

Wani Matashi ya ƙulla tuggun garkuwa da kisan Mahaifin sa a jihar Osun

Hukumar 'yan sanda ta jihar Osun, a ranar Talatar da ta gabata ta bayar da sanarwar cafke wani matashi mai shekaru 27, Isa Adamu, bisa laifi na ƙulla tuggun garkuwa da kuma kisan mahaifin sa dan shekara 55 bayan ya karbe kudin fansarsa.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Fihiman Adeoye, shine ya bayyana hakan yayin gabatar da Matashin da kuma sauran wadanda ke da hannun cikin wannan aika-aika ga manema labarai a babban birnin jihar na Osogbo.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 27 ga watan Afrilun da ya gabata ta wadansu Mutane suka yi garkuwa da Marigayi, Ibrahim Adamu, inda tsayuwar daka ta jami'an tsaro wajen bincike ta damkar masu wannan mummunan shiri da ya riga fata.

Binciken hukumar kamar yadda Adeoye ya bayar da shaida ya tabbatar da cewa, 'da ga marigayi Adamu ya amsa lafin sa na ƙulla tuggun wannan lamari na garkuwa da son abin duniya ya kai shi ga halaka Mahaifin sa.

Wani Matashi ya ƙulla tuggun garkuwa da kisan Mahaifin sa a jihar Osun

Wani Matashi ya ƙulla tuggun garkuwa da kisan Mahaifin sa a jihar Osun
Source: Facebook

A yayin da jami'an tsaro ke tsitsiyar Isa, ya bayyana cewa masu garkuwar sun yi alkwarin ba shi wani kaso na N500, 000 cikin kudin fansar mahaifin sa da tuni suka karbe har N3m, wanda ashe yaudara ce sai N45, 000 kacal ya tashi da ita.

KARANTA KUMA: Mun yi matukar dakusar da Boko Haram a Arewa maso Gabas - Buratai

Ba ya ga karbe kudin fansar, mamuguntan sun kuma hallaka Mahaifin Isa tare da jefa gawarsa cikin wani rafi inda ruwa ya yi gaba da ita da lamarin ya zamto biyu baba a gare sa ta rashin mahaifi da kuma rashin samun dukiyar da ya nufata.

Kazalika jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sandan jihar ta kuma cafke wasu 'yan fashi da makami da suka shahara da addabar al'umma a yankunan Owode, Ede da kuma birnin Osogbo na jihar ta Osun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel