Malaman makaranta da na kiwon lafiya 2,000 suka mutu a shiyyar Arewa maso Gabas

Malaman makaranta da na kiwon lafiya 2,000 suka mutu a shiyyar Arewa maso Gabas

- Kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta ce akalla ma'aikata 2,000 ne rikicin shiyyar Arewa maso Gabas ya lakume rayuwarsu

- Shugaban kungiyar na kasa, Mr. Ayuba Wabba, ya bayyana rashin kyakkyawan muhallin aiki daga cikin dalilan da suka lalata aikin gwamnati

- Ya ce ya zama dole a magance matsalolin tauye hakkin dan Adama da na kungiyoyin kwadago a kasar

Kungiyar hadakar kungiyoyin kwadago ta kasa, a jiya Talata, ta ce rikicin yan ta'adda na Boko Haram ya hallaka akalla ma'aikata 2,00 a shiyyar Arewa maso Gabas, musamman malaman makaranta da na kiwon lafiya, kuma an hallakasu ne a bakin aikinsu.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa, NLC, Mr. Ayuba Wabba, ya bayyana hakan a Abuja a lokacin wani taro na hadin guiwar kungiyar NLC da cibiyar bunkasa aikin kwadago ta kasa da kasa, mai matsugunni a Amurka, AFL-CIO, wanda aka gudanar da nufin samar da hanyoyin zaman lafiya da jin ra'ayoyin jama'ar kasar.

Wabba ya kuma ce idan har yan siyasa suka ci gaba da amfani da siyasa wajen juya hankulan al'umma, to kuwa wannan rikicin ba zai taba yankewa ba.

KARANTA WANNAN: A cikin shekaru 2 zan farfado da tattalin arzikin Nigeria idan aka zabe ni a 2019 - David Mark

Malaman makaranta da na kiwon lafiya 2,000 suka mutu a shiyyar Arewa maso Gabas

Malaman makaranta da na kiwon lafiya 2,000 suka mutu a shiyyar Arewa maso Gabas
Source: Facebook

Ya alakanta rikice rikicen da ke faruwar a kasar, da rashin nagartaccen shugabanci da kuma tauye hakkin bil Adama da na kungiyoyin sa kai, tare da bayyana bukatar cewa samar da ingantaccen shugabanci zai taimaka wajen magance talauci a kasar.

Ya bayyana rashin kyakkyawan muhallin aiki da kuma nuna wariya a wuraren aikin, na daga cikin dalilan da suka lalata aikin gwamnati, wanda ke sawa ba'a ko damuwa da asarar rayukan ma'aikata a bakin aikinsu, yayin da kungiyoyin kwadago ke fuskantar matsaloli na kula da marayu dama zawara na ma'aikatan da aka kashe.

Ya ce: "Dole ne mu magance matsalolin tauye hakkin dan Adama da na kungiyoyin kwadago, musamman ma dai matsalolin da suka shafi shugabanci saboda ganin yadda ta'addanci ke kara ruruwa a yankin Afrika, dama wasu sassa na duniya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel