Mutane 5 na neman EFCC ta basu N49m da aka tsinta cikin buhu

Mutane 5 na neman EFCC ta basu N49m da aka tsinta cikin buhu

Mutane 5 sun gabatar da kansu ga EFCC inda kowannensu ke naman karbar N49m da hukumar da tsinta a ranar 13 ga watan Mayun 2017 a cikin buhu a filin tashin jirage na Kaduna. A yanzu dai hukumar ta gabatar da Shari'ar a babban kotun tarayya na Kaduna domin gano ainihin wanda ke da kudin.

Hukumar yaki da rashawa EFCC ta sanar da cewa mutane biyar sun gabatar da kansu gabanta inda kowanne cikinsu ke ikirarin mallakar zunzurutun kudi N49 miliyan da jami'an hukumar suka tsinta cikin buhu a filin tashin jirage na Kaduna.

A yanzu hukumar ta mika shari'ar kudin ga babban kotun tarayya da ke Kaduna domin gano ainihin wanda ke da kudin.

Mutane 5 na neman EFCC ta basu N49m da aka tsinta cikin buhu

Mutane 5 na neman EFCC ta basu N49m da aka tsinta cikin buhu
Source: Instagram

DUBA WANNAN: Gyaran jadawalin zabe: PDP ta bukaci majalisa ta saka takalmin karfe ta take Buhari

Hukumar ta EFCC ta ce tuni an ajiya kudin a asusun ajiya a bankin kasa CBN kafin kotun ta tabbatar da wanda ke da kudin.

Hukumar ta EFCC ta bayar da wannan sanarwan ne a mujallar da ta ke wallafawa a kowanne wata mai taken "EFCC Alert".

Kamar yadda hukumar ta fadi a mujallar, mutane biyar da suka gabatar da kansu domin karbar kudin sune: Oyebanji Plaits Steve, Taiye Omoniyi Oluwaleke, Risikat Tiamiyu Titilayo, Fausat Oni da Joshua Kisabo.

Idan ba'a manta ba, jami'an EFCC sun gano kudaden ne yayin da ake tattance kayayakin masu tafiya inda aka gano sabbin kudade cikin buhu wanda adadin su ya ka N49 miliyan.

Daga baya wani da yayi ikirarin kudaden nasa ne ya bayyana amma ya kasa fadan adadin kudaden da ke cikin buhun ko gabatar da wata sheda da ke nuna inda ya sama kudaden.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel