Sunaye: An kama rikakkun 'yan fashi a jihohin Arewa 4

Sunaye: An kama rikakkun 'yan fashi a jihohin Arewa 4

Kakakin hukumar 'yan sanda na kasa, Jimoh O. Moshood ya bayar da sanarwar damke wasu kungiyoyin bata gari da suka dade suna aikata fashi da makami, satar motocci, kissan gilla da garkuwa da mutan a titunan Abuja/Kaduna/Birnin Gwari/Funtua da Zamfara.

Kungiyar na farko sun kware ne wajen garkuwa da mutae da fashi da makami

(i) Shefiyu Abdullahi (shugaban kungiya) da (ii) Umar Suleiman wanda akafi sani da Wada

An kama su bayan musayar wuta da 'yan sanda a ranar 16 ga watan Augusta. An kashe uku daga cikinsu yayin musayar wutan. Sun amsa cewa su ne su kayi garkuwa da fitaccen malami Sheikh Mohammed Ahmed Al-garkawi a Kaduna, kuma suka karbi N12 miliyan kafin suka sako shi.

DUBA WANNAN: 'Yan PDP sun kai karar Masari Kotun Koli

Sunaye: An kama rikakkun 'yan fashi a jihohin Arewa 4

Sunaye: An kama rikakkun 'yan fashi a jihohin Arewa 4
Source: Facebook

An kama 'yan kungiya na biyu a ranar 9 ga watan Augustan 2018

(i) Yunusa Musa (Mukoro), (ii) Mohammed Sani (Zandiri), (iii) Mohammed Abubakar (Mujuma), (iv) Umar Sani da (v) Abubakar Mohammed Kata

An kama su da bindigogi 127. Kungiyar sun amsa cewa sun kai hare-hare da dama a jihar Zamfara da Kaduna da Kebbi da Nasarawa da Kogi. Sun aikata laifukan satan shanu, fashi da makami da da garkuwa da mutane a jihohin da aka lissafa.

Sunaye: An kama rikakkun 'yan fashi a jihohin Arewa 4

Sunaye: An kama rikakkun 'yan fashi a jihohin Arewa 4
Source: Twitter

'Yan kunigiya na uku kuma sune wadanda suka yiwa sojojin kwantar bauna suka kashe 11 a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Shugabansu shine Jafaru Alh Adamu da wasu mutane uku da ba'a bayyana sunansu ba sai kuma mutane biyu da suka mutu wajen musayar wuta da jami'an 'yan sanda. An same su da AK47 guda biyu.

Kungiya ta hudu itace ta masu satar motoci da aka kama a Kaduna da Kano, yan kungiyar sun hada da:

(i) Ibrahim Usman aka Sanni, (ii) Ahmed Isah aka Manchi, (iii) Mohammed Abubakar, (iv) Abdulmalik Alhaji (v) Isah Sanni, (vi) Bashir Buda da (vii) Lawal Shuaibu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel