2019: Ba zanyiwa IGBO shamaki da fadar shugaban kasa ba - Bafarawa

2019: Ba zanyiwa IGBO shamaki da fadar shugaban kasa ba - Bafarawa

- Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Attahiru Bafarawa, ya ce zai baiwa kabilar Igbo fifiko idan har ya zama shugaban kasa a 2019

- Attahiru Bafarawa ya ce zai mika ragamar shugabancin kasar ga kabilar Igbo, bayan wa'adin shugabancin sa ya kare.

- Ya ce gwamnatinsa zata kaddamar da tsare tsare da zasu samar da ingantacciyar demokaradiya da kuma hadin kan kasa.

Attahiru Bafarawa, wanda ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya yi alkawarin bada fifiko ga shiyyar Kudu maso Gabas idan har ya samu nasarar lashe zaban shugaban kasa na 2019 da kegabatowa.

Bafarawa, wanda tsohon gwamnan jihar Sokoto ne, ya ce ba wai ya kwallafa ransa na dole sai ya cika wannan kudirin nasa na zama shugaban kasa ba, illa dai kawai cika burinsa na son ganin ya hada kan yan Nigeria.

Da ya ke jawabi a Enugu, a ci gaba da yawon tattaunawa da masu ruwa da tsaki don bashi damar samun tikitin tsayawa takara a jam'iyyar, Bafarawa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na NAN cewar zai mika ragamar shugabancin kasar ga dan asalin kabilar Igbo, bayan wa'adin shugabancin sa ya kare.

KARANTA WANNAN: Yawan barazanar da APC take yi ba zai bata nasara a jihar Kwara ba - PDP

Tsohon gwamnan ya ce zai sanya dukkanin shirye shiryensa a cikin kundi, ta yadda yan Nigeria zasu iya yanke hukunci a kansa idan har ya kasa cika alkawuran da ya dauka.

2019: Ba zanyiwa IGBO shamaki da fadar shugaban kasa ba - Bafarawa

2019: Ba zanyiwa IGBO shamaki da fadar shugaban kasa ba - Bafarawa
Source: Depositphotos

"Na damu kwarai da yadda abubuwa ke tafiya a kasar nan, don haka zan bada fifiko ga samar da hadin kan kasar" a cewar Bafarawa.

"Na riga da na rubuta wani kudi na ayyukan da zan gudanar, ba zan taba daukar alkawarin da nasan ba zan iya cikawa ba. Burina na farko shine hadin kai. Idan har na lashe zabe, zan tafi tare da Igbo tun a ranar farko. Babu tantama akan ayyukan da zanyiwa shiyyar Kudu maso Gabas domin ba zan masu shamaki da fadar shugaban kasa ba.

KARANTA WANNAN: A cikin shekaru 2 zan farfado da tattalin arzikin Nigeria idan aka zabe ni a 2019 - David Mark

"Kasancewa ta tsohon kwararre kan harkokin tattalin arzikin ciki da wajen kasa, da kuma kyakkyawar alakar siyasa, ina da cikakkiyar kwarewa ta samar da nagartacce shugabanci"

Ya ce gwamnatinsa zata kaddamar da wasu tsare tsare da zasu karfafa samar da ingantacciyar demokaradiya da kuma hadin kan kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel