Mun yi matukar dakusar da Boko Haram a Arewa maso Gabas - Buratai

Mun yi matukar dakusar da Boko Haram a Arewa maso Gabas - Buratai

Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, a ranar Talatar da ta gabata ya sake jaddada cewa ko shakka ba bu an dakusar da ta'addancin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Janar Buratai ya jaddada matsayarsa ta dakusar da kungiyar ta'adda ta Boko Haram inda ya bayyana cewa, an dakile aukuwar ta'addancin ta a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan sabanin yadda ake ikirari da babatu.

Buratai ya bayyana hakan ne a yayin bikin karin girma ga dakarun soji 55 a barikin Jaji dake jihar Kaduna, inda shugaban hafsin sojin kasa na kasar Afirka ta Kudu, Laftanar Janar Lindile Yam ya halarta.

Mun yi matukar dakusar da Boko Haram a Arewa maso Gabas - Buratai

Mun yi matukar dakusar da Boko Haram a Arewa maso Gabas - Buratai
Source: Depositphotos

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya kwanaki kadan da suka gabata ya ruwaito cewa, ana ci gaba da yada jita-jitar aukuwar hare-hare kan dakarun soji a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan da cewar rayukan da dama daga cikin su sun salwanta.

KARANTA KUMA: 2019: Wasu Gwamnonin PDP 5 na neman ƙulla yarjejeniya da Shugaba Buhari

Sai dai jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar sojin ta musanta wannan jita-jita ta aukuwar hari da kuma salwantar rayukan dakarun ta kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Kazalika shugaban sojin ya jaddada cewa, hukumar sojin ta ci gaba da jajircewa kan dabbaka wasu dabaru da tsare-tsare na ganin bayan ta'addancin Boko Haram da sanadin goyon baya na shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma al'ummar kasar nan ta gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel