Muna maraba da matakin PDP – Kwankwasiyya

Muna maraba da matakin PDP – Kwankwasiyya

- Siyasar Kano ya dauki wani sabon salo

- Jam'iyyar PDP ta rushe shugabancin jam'iyyar reshen jihar Kano inda ta sanar da yunkurin kafa kwamitin rikon kwarya

- Hakan bai yiwa bangaren Shekarau dadi ba

- Sai dai bangaren Sanata Rabiu Kwankwaaso sun yi maraba da wannan mataki na uwar jam'iyyar PDP

Lamuran siyasa a jihar Kano sun dauki wani sabon salo a farkon watan Satumba bayan uwar jam'iyyar ta kasa ta bada sanarwar rushe shugabancin jam'iyyar reshen jihar.

Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce za a nada kwamitin rikon jam'iyyar, to sai dai har kawo yanzu babu wani bayani game da nadin kwamitin, da kuma wadanda za su jagoranci jam'iyyar.

Matakin dai ya zo wa wasu mutane ba-zata, saboda babu wani laifi da aka tuhumi zababbun shugabannin da aikatawa, kuma babu wani da ya ke kalubalantar shugabancinsu.

Muna maraba da matakin PDP – Kwankwasiyya

Muna maraba da matakin PDP – Kwankwasiyya
Source: Twitter

Sai dai hasashe sun nuna cewa manyan jam'iyyar suna da masaniyar cewa hakan za ta iya afkuwa, kuma ma sun ga alamun hakan, tun bayan sauya shekar tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso daga APC zuwa PDP.

Tsofaffin 'yan jam'iyyar musamman bangaren tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau sun yi watsi da matakin, inda suka bayyana cewa hakan tsagwaron rashin adalci ne.

KU KARANTA KUMA: Bamu tsayar da kowani dan takaran shugaban kasa ba – Afenifere sun maida martani ga rahoton tsayar da Buhari

Bangaren tsohon gwamna Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso murna suka yi da matakin, suka kuma karbe shi hannu, biyu-biyu, saboda za a ba su wani bangare na shugabancin jam'iyyar.

Wani babban na hannun daman Kwankwaso Kwamared Aminu Abdussalam ya bayyana cewa, bai kamata wasu 'yan jam'iyyar su nuna rashin gwamsuwa da matakin rusa shugabannin ba, a cewarsa kamata ya yi su mika wuya, su kuma amince da duk abinda zai biyo baya.

A halin da ake ciki, Malam Ibrahim Shekarau a wani jawabi da mu ka samu daga Magoya bayan sa, ya tabbatar da cewa babu gaskiya a cikin jita-jitar da ake yadawa cewa ya bar PDP.

Tsohon Gwamnan yace kawo yanzu yana nan a babbar Jam’iyyar adawar kasar.

Ibrahim Shekarau wanda yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP yace ba su yi na’am da rusa shugabancin PDP da aka yi a Kano ba kuma tuni su ka maka uwar Jam’iyya kara a gaban wani Kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel