Bamu tsayar da kowani dan takaran shugaban kasa ba – Afenifere sun maida martani ga rahoton tsayar da Buhari

Bamu tsayar da kowani dan takaran shugaban kasa ba – Afenifere sun maida martani ga rahoton tsayar da Buhari

Kungiyar Afenifere a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba ta karyata ikirarin cewa ta tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma wani dan takara a zaben 2019.

Kungiyar tace rahotannin cewa shugabannin Afenifere sun tsayar da wani dan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa karya ne.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar tace a yanzu sun mayar da hankali wajen tattaunawa day an takaran shugaban kasa tare da kokarin tabbatar da ganin an sake fasalin Najeriya zuwa mai inganci.

Bamu tsayar da kowani dan takaran shugaban kasa ba – Afenifere sun maida martani ga rahoton tsayar da Buhari

Bamu tsayar da kowani dan takaran shugaban kasa ba – Afenifere sun maida martani ga rahoton tsayar da Buhari
Source: Facebook

Afenifere a wata sanarwa daga Reube Fasoranti tace a yanzu ta na kokarin ganin ta cimma ceto Najeriya daga halaka.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta kai karar gwamnatin Najeriya ga manyan kasashen Turai guda 2

A wani lamari na daban, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Jam’iyyar a tsarin gudanarwan tat ace za’a samar dad an takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct”kenan a turance.

Ta kuma sanya zaben fidda gwani na gwamnoni zai gudana a ranakun Litinin, 24 ga watan Satumba da 25 ga watan Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel