APC ta rage farashin fam din takara, tayi alkawarin fitar da dan takaran shugaban kasa a ranar Alhamis

APC ta rage farashin fam din takara, tayi alkawarin fitar da dan takaran shugaban kasa a ranar Alhamis

- APC ta sanya ranakun zaben fidda gwani

- Jam’iyyar a tsarin gudanarwan tat ace za’a samar dad an takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani

- Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa duk dan takaran kujerar shugaban kasa zai mallaki fam akan naira miliyan 45

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya ranar zaben fidda gwani na shugaban kasa domin zabar dan takaranta a zaben shugaban kasa na 2019.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sunce zaben fidda gwani na jam’iyyar mai mulki zai gudana a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Jam’iyyar a tsarin gudanarwan tat ace za’a samar dad an takarar shugaban kasa ta hanyar zaben fidda gwani wato “direct”kenan a turance.

Ta kuma sanya zaben fidda gwani na gwamnoni zai gudana a ranakun Litinin, 24 ga watan Satumba da 25 ga watan Satumba.

APC ta rage farashin fam din takara, tayi alkawarin fitar da dan takaran shugaban kasa a ranar Alhamis

APC ta rage farashin fam din takara, tayi alkawarin fitar da dan takaran shugaban kasa a ranar Alhamis
Source: Depositphotos

APC a wata sanarwa daga sakataren tsare-tsarenta, Emma Ibediro, APC ta kuma nuna cewa za’a fara siyar da fam din tsayawa takara a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa duk dan takaran kujerar shugaban kasa zai mallaki fam akan naira miliyan 45 inda aka rage naira miliyan 10 kan yadda yake a baya.

APC ta kuma bayyana cewa yan takaran kujerar gwamna zasu yanki fam akan naira miliyan 22.5.

Yayinda yan takaran kujerar sanata zasu yank fam naira miliyan 7. Inda yan majalisar wakilai zasu yanki nasu akan naira miliyan 3.85.

KU KARANTA KUMA: Ba zan dauki mataki ba sai na tuntubi mutane na – Shekarau

Har ila yau yan majalisar dokoki na jiha zasu biya N850,000.

Sannan kuma ana sanya ran yan takara mata da nakasassu zasu biya kaso 50 na kudin kowani matsayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel