Ba zan dauki mataki ba sai na tuntubi mutane na – Shekarau

Ba zan dauki mataki ba sai na tuntubi mutane na – Shekarau

A jiya kun ji labari cewa cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP ya koma APC. Babban ‘Dan siyasar ya karyata wannan rade-radin inda yace bai bar PDP ba tukuna.

Ba zan dauki mataki ba sai na tuntubi mutane na – Shekarau

Shekarau bai fitar da matsaya game da barin PDP ba
Source: Depositphotos

Malam Ibrahim Shekarau a wani jawabi da mu ka samu daga Magoya bayan sa, ya tabbatar da cewa babu gaskiya a cikin jita-jitar da ake yadawa cewa ya bar PDP. Tsohon Gwamnan yace kawo yanzu yana nan a babbar Jam’iyyar adawar kasar.

Ibrahim Shekarau wanda yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP yace ba su yi na’am da rusa shugabancin PDP da aka yi a Kano ba kuma tuni su ka maka uwar Jam’iyya kara a gaban wani Kotu.

KU KARANTA: Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai yi kokarin jawo Shekarau

Wannan abu da Jam’iyyar PDP tayi ne ya jawo Shekarau da Magoya bayan sa da sauran manyan ‘Yan siyasar Kano su ka fusata. Shekarau yace yanzu haka yana cigaba da tuntubar mutanen sa game da yiwuwar sauya sheka daga PDP.

Tsohon Gwamnan a wannan jawabi da yayi, ya bayyana cewa babu yadda za ayi ya dauki wani mataki a siyasa ba tare da ya zauna da Mabiyan sa ba. Ana dai sa rai cikin ‘yan kwanakin nan a jiya matsayar ‘Dan takarar Shugaban kasar.

Saurari cikakken jawabin Malam Shekarau yana karyata abin da Hadimin sa ya bayyana a baya

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel