Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya Paul Arkwright ya ziyarci Kwankwaso

Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya Paul Arkwright ya ziyarci Kwankwaso

Labari ya zo mana cewa babban Jakadan Kasar Ingila a Najeriya ya kai wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ziyara a gidan sa da ke Unguwar Maitama a cikin babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja.

Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya Paul Arkwright ya ziyarci Kwankwaso

Paul Arkwright tare da Kwankwaso a Garin Abuja Hoto daga: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa sun gana da Paul Arkwright ne jiya da yamma a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita. Kwankwaso yace sun zauna ne kan batutuwan da su ka shafi kasashen 2.

Tatattaunawar Sanatan da kuma babban Wakilin na Kasar Birtaniya a Najeriya ta shafi alakar da ke tsakanin Najeriya da kuma babbar kasar ta Turai. Yanzu haka Tsohon Gwamnan yana cikin masu neman takarar Shugaban kasa a 2019.

KU KARANTA: Tsohon IGP zai fito takarar Sanata a Jam'iyyar APC

‘Dan takarar Shugaban Kasar ya nuna cewa ya ji dadin wannan ganawa da su kayi yana mai farin cikin karbar ziyarar wannan babban Jakada na Kasar waje. Kwanan nan ne Kwankwaso ya dawo gida bayan ya kai ziyara Jihar Abia.

Mun dai kuma samu labari cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai wa Edwin Clark ziyara bayan ‘Yan Sanda sun yi masa kutse a cikin gida. Clark tsohon Ministan Najeriya ne kuma yana cikin Dattawan Yankin Neja-Delta a Kudu.

Jiya kun ji cewa Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo ya ja kunnen Jam’iyyar PDP wajen tsaida ‘Dan takaran 2019 inda yace kayi wa PDP duk wani fadi-tashi don haka dole ayi la’akari da su kafin a duba wadanda su ka sauya-sheka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel