Jam’iyyar PDP ta kai karar gwamnatin Najeriya ga manyan kasashen Turai guda 2

Jam’iyyar PDP ta kai karar gwamnatin Najeriya ga manyan kasashen Turai guda 2

A daidai lokacin da zabukan shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, jam’iyyun na ta fito da sababbin tsurfa da dabarun neman jama’a su jiyo amonsu tare da bukatar ganin sun bata sunayen abokan hamayyarsu ko hakan zai basu damar samun kuri’u.

Anan ma jam’iyyar PDP ce ta aika da wata doguwar waraka ga shugaban kasar Jamus, Angela Merkel da shugaban kasar Birtaniya, Theresa May, inda a cikinsa ta shigar da karar jam’iyyar APC a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Najeriya ce kasa ta 43 a cikin kasashen Duniya da suka fi karfin Soja

Jam’iyyar PDP ta kai karar gwamnatin Najeriya ga manyan kasashen Turai guda 2

Secondus
Source: Depositphotos

PDP ta fada ma shuwagabannin biyu mata cewa gwamnatin APC na amfani da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC wajen farautar abokan hamayya, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Wasikar da aka shiryata a ranar 30 ga watan Agusta ta samu sa hannun shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, kuma ya bayyana ma shuwagabannin kasashen cewa APC ta mayar da Najeriya wkasa

“EFCC ta mayar da bincike kamar wani tabbacin aikata laifi, inda take watsa maganan bincke a kafafen watsa labaru don ta bata ma wanda ake binciken suna, wadanda yawancinsu shuwagabanni ne a PDP, wadanda ake ganinsu kamar barazana ne ga gwamnatin APC.

“Bugu da kari APC ta yi amfani da EFCC wajen rufe asusun bankin jihar Benuwe da na jahar Akwa Ibom, ta tabbata yaki da rashawa da shugan kasa Muhammadu Buhari ke ikirarin yi ya zama shirme, tunda dai jam’iyyar PDP kadai ake hari.” Inji Uche Secondus.

Daga karshe PDP ta yi kira ga shuwagabannin biyu dasu gaggauta shiga cikin wannan maganar, don kawar da aukuwar mummunan tashin hankali a Najeriya da ka iya janyoasarar rayuka da dukiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel