Uwar jam’iyyar PDP ta sake rushe kwamitin rikon jam’iyyar a Kano

Uwar jam’iyyar PDP ta sake rushe kwamitin rikon jam’iyyar a Kano

Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta sake rushe kwamitin riko da ta kafa a jihar Kano don sake fadada shi domin ya kunshi kowanne bangare na magoya bayan tsofin gwamnonin jihar; Rabi’u Musa Kwankwaso da Ibrahim Shekarau.

A yau, Talata, ne wani hadimin, Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana cewar Shekarau din ya koma APC kafin daga bisani ya tsohon gwamnan ya musanta hakan.

Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya shaiadawa Daily Nigerian cewar Shekarau bai fita daga jam’iyyar PDP ba domin bai aiko masu a rubuce ba.

Uwar jam’iyyar PDP ta sake rushe kwamitin rikon jam’iyyar a Kano

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa; Uche Secondus
Source: Depositphotos

Ya ce jam’iyyar ta tuntubi tsohon gwamnan a yau kuma ya tabbatar masu cewar har yanzu yana jam’iyyar PDP.

DUBA WANNAN: 2019: Atiku ya fadi bakaken maganganu a kan Buhari

Ologbondian ya kara da cewar jam’iyyar PDP a shirye take ta saurari korafi ko wata shawara da duk wani mamba a jam’iyyar zai bayar muddin domin zasu haifar da sulhu da zaman lafiya.

Shugabancin jam’iyyar ya tabbatar da cewar ba zasu taba yin shakulacin bangaro da korafin ‘ya’yanta a jihar ta Kano ba.

Kazalika ta bawa dukkan ‘ya’yanta a jihar ta Kano tabbacin cewar zata yi tafiya da kowa domin ganin an gudu tare an tsira tare4.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel