Jami’an hukumar yaki da fasakauri zasu fara bin gidajen jama’a don kwato haramtattun shinkafa

Jami’an hukumar yaki da fasakauri zasu fara bin gidajen jama’a don kwato haramtattun shinkafa

Nan gaba kadan jami’an hukumar kwastam zasu fara bin gida gida don binciko haramtattun shinkafa da aka shigo dasu ta barauniyar hanya tare da kamasu, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar zata fara daukan wannan mataki ne a jahar Ogun, jahar da suka ce ake yawan samun shigowar haramtattun kayayyakin da gwamnatin Najeriya ta hana shigowa dasu.

KU KARANTA: Fitaccen musulmin dan kwallon Duniya ya wanke bandakin masallaci a Ingila

Kwanturolan kwastam na yankin jahar Ogun, Michael Agbara ne ya bayyana haka yayin dayake zantawa da yan jaridu a iyakar Najeriya da Bini, Idiroko, inda yace wannan mataki yayi daidai da tsarin gwamnatin tarayya na habakka noman shinkafa a Najeriya.

Jami’an hukumar yaki da fasakauri zasu fara bin gidajen jama’a don kwato haramtattun shinkafa

Kwastma
Source: Depositphotos

Agbara yace wannan sabon tsarin nasu ya kunshi binciken gida gida da manyan wararen ajiyan kaya nay an kasuwa don kwato haramtattun shinkafa, haka zalika yace wannan mataki nada goyon bayan dokokin hukumar kwastam.

“Ina tabbatar muku mun ja tunga, kuma zamu cigaba da yakar masu fasakuri don kawo karshen fiton haramtattun kaya zuwa kasa Najeriya, ko ka boye a gidanka, ko ka boye shine a babban suto sai mun kwacesu, don haka jami’an sun shirya tsaf don fara wannan aiki.” Inji shi.

Bugu da kari Agbara yace sun kwace buhuna shinkafa dubu shida da dari da casa’in da hudu (6,194) fda aka shigo dasu ba akan ka’ida ba, da galolin man gyada guda dari uku da casa’in da biyar (395), dilan gwanjo guda bakwai, galan dari uku da arba’in (340) na man fetir da katan 45 na lemun kwalba, duk a watan Agustan daya gabata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel