2019: Zan marawa duk dan takaran da ya samu tikitin takara na PDP baya - Bafarawa

2019: Zan marawa duk dan takaran da ya samu tikitin takara na PDP baya - Bafarawa

Alhaji Attahiru Bafarawa, dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sha alwashin marawa duk dan takaran da yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar domin zaben 2019.

Hakan zai kasance ne idan har ya gaza samun tikitin tsayawa jam’iyyar a matsayin dan takara a zabe mai zuwa.

Bafarawa, wadda ya kasance tsohon gwamnan jihar Sokoto ya yi wannan alkawarin ne a ranar Talata, 4 ga watan Satumba yayinda ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna David Umahi a kokarinsa na bayyana kudirinsa na takara.

2019: Zan marawa duk dan takaran da ya samu tikitin takara na PDP baya - Bafarawa

2019: Zan marawa duk dan takaran da ya samu tikitin takara na PDP baya - Bafarawa
Source: Depositphotos

Sai dai yace ya zama dole a tantance su kafin a yanke shawarar zabar dan takaran da zai tsayawa jam’iyyar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Bafarawa ya kaddamar da cewa babu mai iya shugabantar Najeriya ba tare da ya taba tarin ilimi da kasuwancin Ndi Igbo ba.

Ya bayyana hakan a lokacin da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya karbi bakuncinsa a Enugu a ranar Talata, 4 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Ni ba barawo bane – Atiku Abubakar

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ya je Enugu ne domin tattaunawa tare da sanar da jam’iyyar a jihar game da kudirinsa na takarar kujerar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

Ya roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da anyi zabe mai inganci da gaskiya a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel