Kungiya tayi karar Saraki da Akpabio kan sauyin sheka

Kungiya tayi karar Saraki da Akpabio kan sauyin sheka

- Kungiyar wayar da kan mutane tayi karar 'yan majalisa da suka sauya sheka a kotu

- Kungiyar na bukatar kotu ta sauke 'yan majalisar daga kujerunsu domin kuma a sake zaben maye gurabensu

- Kungiyar ta bayar da misalai yadda wasu 'yan majalisun johihi suka rasa kujerunsu bayan sauya sheka

Wata kungiya mai wayar da kan jama'a, Enough is Enough (EiE) Nigeria, ta shigar da kara a babban kotun Abuja inda ta ke bukatar kotu da kori dukkan 'yan majalisa da suka sauya sheka domin a gudanar da zabin maye gurabensu.

Wasu daga cikin 'yan majalisan da suka sauya sheka sun hada da shugaban majalisa Bukola Saraki da tsohon shugaban marasa rinjaye, Godswill Akpabio. A yayin da Saraki ya sauya sheka daga APC zuwa PDP, Akpabio ya yi kishiyar hakan.

Kungiyoyi sun hada kai don kai Saraki da Akpabio kara kan sauyin sheka

Kungiyoyi sun hada kai don kai Saraki da Akpabio kara kan sauyin sheka
Source: Depositphotos

A karar da kungiyar ta shigar mai lamaba FHC/ABJ/CS/923/2018 a ranar 28 ga watan Augustan 2018, kungiyar ta ce 'yan majalisar sun fice daga jam'iyyun da suka basu inuwar takara kuma su kayi nasara ba tare da rabuwan kai a jam'iyyar ba.

DUBA WANNAN: Barayin gwamnati sun fara birne kudade a makabartu da gidajen karkashin kasa - Gwamnan PDP

Kungiyar ta ce dan majalisa yana iya cigaba da kasancewa a kujerarsa ne bayan sauya sheka idan jam'iyyarsa ta rabu kashi biyu kamar yadda ta faru a shari'ar Abegunde da majalisar jihar Ondo a 2015.

Kungiyar kuma ta bayar da misalin abinda ya faru a majalisar jihar Kaduna inda Kakakin majalisar ya sanar da cewa za'a gudanar da zaben maye gurbin wasu 'yan majalisa biyu da suka sauya sheka. "Muna son a cigaba da daukan irin wannan matakin a dukkan jihohin Najeriya da babban birnin tarayya.

A halin yanzu ba'a tsayar da ranar sauraron karar ba saboda ba'a mika shari'ar ga alkalin da zai saurare ta ba.

Shugaban tsare-tsare na kungiyar, Dapo Awobekun ya bukaci a kotun tayi gagawar fara sauraron shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel