Yanzu Yanzu: Har yanzu ina a PDP - Shekarau

Yanzu Yanzu: Har yanzu ina a PDP - Shekarau

- Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim shekarau, ya ce shi bai sauya sheka daga PDP ba

- Hadimin dan takaran kujerar shugaban kasar ne ya sanar da batun ficewar nasa

- Sai dai ya karyata hakan a shafinsa na twitter

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takaran kujerar shugaban kasa, Mallam Ibrahim shekarau, ya ce shi bai sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba kamar yadda rahotanni ke nunawa.

A safiyar yau Talata, 4 ga watan Satumba ne hadimin Shekarau akan kafofin watsa labarai, Sule Ya’u Sule ya sanar da rashin amincewarsu da abin da ya kira “rashin adalci" da ake masu daga hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Rahotanni da dama sun ruwaito Sule yana mai bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar bisa wannan dalili.

Posts ai ai shafin zumuntan tsohon gwamnan na Twitter ya nuna cewa yana nan daram-dakam bai fita daga jam’iyyar ta PDP ba.

KU KARANTA KUMA: Zamu tsige Saraki a matsayn shugaba, sannan mu fatattake shi daga majalisar dattawa – Omo-Agege

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel