2019: Wasu Matasa sun nemi APC tayi amfani da ‘yar tinke wajen zaben ‘Yan takara

2019: Wasu Matasa sun nemi APC tayi amfani da ‘yar tinke wajen zaben ‘Yan takara

Wasu Matasa da ke goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari sun yi zanga-zanga a babban ofishin Jam’iyyar APC kwanan nan su na masu kira ayi amfani da zaben ‘yar tinke wajen zaben ‘Yan takarar Jam’iyyar a zaben 2019.

2019: Wasu Matasa sun nemi APC tayi amfani da ‘yar tinke wajen zaben ‘Yan takara

Wasu Matasa sun yi zanga-zangar lumana a Hedikwatar APC
Source: UGC

Yusuf Ardo wanda shi ne Kakakin wannan Kungiya ya nemi Jam’iyyar APC tayi watsi da yadda ta saba gudunar da zaben fitar da gwani ta gudanar da zabe kato-bayan-kato a bana. Malam Ardo yace hakan ne zai ba Talakawa karfi a kasar nan.

Matasan sun nemi Shugaban APC ya tsaya kan bakan sa na canza tsarin tsaida ‘Dan takarar da zai rikewa Jam’iyya tuta. Haka kuma Matsan sun nuna takaicin su ga Gwamnonin APC da ke kokarin ganin an cigaba da aiki da tsarin da aka saba.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta fara shiryawa zaben Gwamnan Jihar Osun

Wannan Kungiya da ke tare da Buhari da Osinbajo tace tsarin da ake tafiya a kai bai ba marasa karfi damar yin nasara wajen samun tutar Jam’iyya. Shugaban wannan Kungiya Hajia Fatimah Gohi ta halarci wannan zanga-zanga jiya.

Dama kun ji cewa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa watau Adams Oshiomhole ya nuna cewa ba za ayi zaben kato-bayan-kato wajen fitar da ‘Yan takara a Jihar Adamawa ba bayan wasu na-kusa da Gwamnan Jihar sun yi bore.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel