2019: Ba za mu zabi Atiku da Buhari ba - Wata Kungiyar Mata ta sha alwashi

2019: Ba za mu zabi Atiku da Buhari ba - Wata Kungiyar Mata ta sha alwashi

Wata Kungiyar Matan Arewa ta Kaduna Women Network Consultative Forum, ta sha alwashin cewa ba za ta zabi daya daga cikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba na jam'iyyar APC ko kuma tsohon shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Kungiyar kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito ta bayyana cewa, ba za ta zabi daya daga cikin shugabannin biyu ba sakamakon ba bu abinda zasu tsinanawa mata a kasar nan.

A madadin haka kungiyar yayin taron da ta gudanar cikin Birnin Kaduna a yau Talata ta bayyana cewa, gwara ta hada kanta wuri guda domin marawa kowace Mace da duk wata jam'iyyar siyasa za ta tsayar takara a kasar nan.

Jagorar wannan kungiya, Zulai Shehu Bello, ita ta bayyana wannan hukunci da suka yanke yayin ganawa da manema labarai dangane da taron yini guda na wayar da kan Mata akan zaben 2019 da kungiyar ta gudanar.

2019: Ba za mu zabi Atiku da Buhari ba - Wata Kungiyar Mata ta sha alwashi

2019: Ba za mu zabi Atiku da Buhari ba - Wata Kungiyar Mata ta sha alwashi
Source: Depositphotos

A cewar Hajiya Zulai, Mata na da kashi na shugabanci da hakan zai sanya su jajirce wajen hada kan su domin ganin Macen da ta cancanta ta zamto shugabar kasar nan ta Najeriya a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Wani Matashi ya sheme Mahaifiyarsa da Katako a jihar Legas

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar tun kafurwarta take kai ruwa rana tare da jajircewa dangane da yadda maza suka rinjayi siyasar kasar nan, inda take neman Mata suka karbi ragamar jagoranci a kasar nan.

Kazalika Zulai ta jaddada cewa, kungiyar ta gudanar da wannan taro ne domin wayar da kawunan mata dangane da muhimmanci su na goyon bayan 'yan uwan su na jinsi babban zaben 2019 na kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel