Mu mu kayi wa PDP duk wani fadi-tashi don haka dole ayi la’akari da mu - Dankwambo

Mu mu kayi wa PDP duk wani fadi-tashi don haka dole ayi la’akari da mu - Dankwambo

Labari ya zo mana cewa daya daga cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP watau Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo yayi wani kira ga babban Jam’iyyar adawar kasar.

Mu mu kayi wa PDP duk wani fadi-tashi don haka dole ayi la’akari da mu - Dankwambo

Mu mu kayi wa Jam’iyya biyayya a PDP – Gwamna Dankwambo
Source: Depositphotos

Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo ya ja kunnen Jam’iyyar PDP inda yace ta fara duba wadanda su ka jajirce a Jam’iyyar ta PDP wajen tsaida ‘Dan takaran ta na Shugaban kasa a zaben 2019.

Ibrahim Dankwambo wanda yana cikin masu neman tikitin takara a karkashin lemar PDP ya bayyana cewa su ne su ka tsaya tare da PDP lokacin da kowa ya watse don haka dole a lura da wannan.

KU KARANTA: Dole 'Dan takara ya dama da Inyamurai - Bafarawa

Dr. Dankwambo yayi wannan jawabi ne a shafin sa na Tuwita kwanakin baya. Bayan nan kuma Gwamnan na PDP ya bayyana cewa ya gina tituna na tsawon kilomita 1600 a Jihar Gombe daga 2011.

Kwanaki ne dai Gwamnan ya leka Kudancin Najeriya inda yake neman kuri’un ‘Ya ‘yan PDP a wajen zaben fitar da gwani da za ayi nan gaba. Gwamnan ya ji dadin tarbar da mutanen Imo su kayi masa.

Kun ji labari a baya cewa Dankwambo ya fito ya nuna cewa shi ya cancanta a zaba a Najeriya a zabe mai zuwa domin kuwa yana da Digiri fiye da 10 don haka ya san yadda zai magance matsalolin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel