Bafarawa yace babu shugaban kasar da zai iya cimma nasara ba tare da yan Igbo ba

Bafarawa yace babu shugaban kasar da zai iya cimma nasara ba tare da yan Igbo ba

- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa yace babu shugaban kasar da zai iya cimma nasara ba tare da yan Igbo ba

- Bafarawa dai ya nuna aniyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa karkashin PDP

- Ya roki Bhugaba Buhari da ya tabbatar da anyi zabe na gaskiya da amana a 2019

Alhaji Attahiru Bafarawa, dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya kaddamar da cewa babu mai iya shugabantar Najeriya ba tare da ya taba tarin ilimi da kasuwancin Ndi Igbo ba.

Bafarawa, wadda ya kasance tsohon gwamnan jihar Sokoto ya bayyana hakan a lokacin da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya karbi bakuncinsa a Enugu a ranar Talata, 4 ga watan Satumba.

Bafarawa yace babu shugaban kasar da zai iya cimma nasara ba tare da yan Igbo ba

Bafarawa yace babu shugaban kasar da zai iya cimma nasara ba tare da yan Igbo ba
Source: Depositphotos

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ya je Enugu ne domin tattaunawa tare da sanar da jam’iyyar a jihar game da kudirinsa na takarar kujerar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

Ya roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da anyi zabe mai inganci da gaskiya a 2019.

KU KARANTA KUMA: Dubi Ronke Ajayi wacce ta sha alwashin siyar da dukkanin abunda ta mallaka don siyawa Buhari fam din takara

Bafarawa yace Shugaba Buhari bai da zabin da wuce tabbatar da zabe mai inganci domin shima ya amfana daga hakan a baya.

Ya kuma yabama Gwamna Uguwanyi da PDP na jihar kan irin kyakyawar tarban day a samu sannan yayi alkawarin tafiya tare da kowa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel