APC za tayi wani baban taro domin shiryawa zaben 2019

APC za tayi wani baban taro domin shiryawa zaben 2019

Yanzu haka, Jam'iyyar PDP tana ta yin wani taro na musamman a makon nan domin duba farashin fam din da tsaida na ‘Yan takara. Mutane da dama sun koka da cewa APC ta tsawwala kudin sayen fam din.

APC za tayi wani baban taro domin shiryawa zaben 2019

Wani babban taron APC da aka shirya kwanakin baya
Source: Twitter

Mun samu labari cewa taron da Jam’iyyar APC ke yi ya shiga rana ta biyu bayan da Majalisar aiwatarwa ta NWC dage zaman ta zuwa yau. Jam’iyyar tayi hakan ne domin wasu manyan ‘Ya ‘yan ta su halarci taron shirin zaben Gwamna a Osun.

Jam’iyyar ta zauna a jiya Litinin ne domin batutuwan da su ka shafi zaben 2019 inda aka nemi a rage farashin fam din tsayawa takarar zaben fitar da gwani. Bayan nan kuma Jam’iyyar za ta fitar da yadda za ta ba ‘Yan takara tuta a zaben 2019.

KU KARANTA: Wani 'Dan takarar Gwamna a Kwara ya fice daga PDP

Abbas Braimah wanda shi ne babban Hadimin Shugaban APC na kasa ya nuna cewa sun dauki matakin cewa ba za ayi zaben kato-bayan-kato wajen fitar da ‘Yan takara a Jihar Adamawa ba. Ana sa rai yau za a cigaba da wannan babban taro.

Jam’iyyar APC din na kokarin cin ma matsaya game da hanyar da za a bi wajen tsaida ‘Yan takara. Wasu Magoya bayan Shugaban kasa Buhari dai sun yi zanga-zangar lumana a Hedikwatar Jam’iyyar APC inda su ke yi wa Gwamnoni bore.

Yanzu haka dai Jam’iyyar APC mai mulki na kokarin maida fam din takarar Sanata ya zama Naira Miliyan 8.5 yayin da na Majalisar dokoki zai koma Miliyan 1.5 yayin da ita kuma Jam’iyyar PDP za ta rangwantawa mata da matasa takara a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel