EFCC: Dudafa yace ba shi da hannu a zargin satar Biliyan 1.6

EFCC: Dudafa yace ba shi da hannu a zargin satar Biliyan 1.6

Waripamo-Owei Dudafa wanda shi ne mai ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan kan harkokin cikin gida ya karyata zargin da Hukumar EFCC ta daura masa na satar wasu makudan kudi.

EFCC: Dudafa yace ba shi da hannu a zargin satar Biliyan 1.6

Dudafa yace kudin coci EFCC ta ke zargin sa da dauka
Source: Original

Labari ya iso mana cewa Waripamo-Owei Dudafa wanda yana cikin ‘Yan fadar tsohon Shugaban kasa Jonathan yace kudin da ake zargin sa da yin awon-gaba da su ba na sa bane. Dudafa yace wani coci ne ya tara wannan makudan kudi a shekarar 2013.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa tana zargin Waripamo-Owei Dudafa da satar kudin da su ka haura Naira Biliyan 1.6. Dudafa ya bayyanawa Kotu cewa wani cocin Angilika ce ta tara kudin da ake same sa da su.

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo ya leko Jami'ar Bayero

Tsohon mai ba Shugaban kasar shawara ya bayyana cewa kudin da su ke yawo a asusun sa, gudumuwa ce da Prince Arthur Eze da kuma wasu Bayin Allah su ka tarawa wani babban coci a Legas. Eze kurum ya bada gudumuwar Dala Miliyan 10 a lokacin.

Dudafa ya fadawa Kotu cewa tsohon Shugaban kasa Jonathan yana cikin manyan wannan coci. Yanzu haka dai ana shari’ar a babban Kotun Tarayya da ke Legas. Dudafa yace ‘yan uwa da abokan arziki ne su ka kafa gidauniya na coci har aka tara wannan kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel