A cikin shekaru 2 zan farfado da tattalin arzikin Nigeria idan aka zabe ni a 2019 - David Mark

A cikin shekaru 2 zan farfado da tattalin arzikin Nigeria idan aka zabe ni a 2019 - David Mark

- Tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark, ya sha alwashin gyara tattalin arzikin kasar cikin shekaru biyu idan har yan Nigeria suka bashi dama

- David Mark, wanda ya sayi tikitin tsayawa takatrar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a yau Talata, ya ce ya mallaki siffofin shugaban da zai kai kasar ga tudun mun tsira

- David Mark zai yi takara a zaben fitar da gwani a jam'iyyar PDP da akalla mutane 10 da suka nuna sha'awar tsayawa takarar

Tsohon shugaban majalisar dattijai ta kasa David Mark ya shiga sahun wadanda suka bayyana kudurinsu na tsayawa takarar shugaban kasa a 2019, yana mai alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar a cikin shekaru biyu.

Da ya ke yin jawabi ga shuwagabannin jam'iyyar ta PDP a lokacin da ya karbi tikitin tsayawa takara, a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja, a ranar talata, Mark ya ce yan Nigeria su duba rawar da ya taka a lokacin da ya ke aikin soji wajen duba cancantarsa na shugabancin kasar.

Ya yi ritaya daga rundunar sojin kasa yana da matsayin Birgdiya Janar.

Mark ya ce idan aka yi la'akari da yawan mutanen da suka sayi tikitin tsayawa takara a jam'iyyar, "ko da wannan, za'a iya cewa PDP ce ake so a kasar".

KARANTA WANNAN: APC ta bayyana dalilin da yasa ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani

Zan farfado da tattalin arzikin Nigeria a cikin shekaru biyu - David Mark

Zan farfado da tattalin arzikin Nigeria a cikin shekaru biyu - David Mark
Source: Facebook

Daga cikin wadanda suka sayi tikitin tsayawa takarar shugaban kasar a PDP sun hada da: Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki; tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto; Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, da dai sauransu.

"A cikin shekaru biyu, idan har kuka bani dama, zan farfado da tattalin arzikin kasar, zamu magance matsalolin tsaro, zamu tabbatar da mun hada kan yan kasar. Rashin yarda a cikin gwamnati ya dade yana ciwa kasar tuwo a kwarya.

"Ina da kyakkyawan horo a aikin soji, haka zalika, na shiga siyasa tun a shekara ta 1998. Ina tsammanin zuwa yanzu, na mallaki dukkanin siffofin da ake bukata, na shugaban da zai kai kasar ga tudun mun tsira

"Maganar gaskiyan shine, akwai muhimman wuraren da ya kamata a duba, sake fasalin kasar na daya daga cikinsu. Ina tunanin lokaci yayi da ya kamata mu sake fasalin kasar nan" a cewar David Mark.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel