Zamu tsige Saraki a matsayn shugaba, sannan mu fatattake shi daga majalisar dattawa – Omo-Agege

Zamu tsige Saraki a matsayn shugaba, sannan mu fatattake shi daga majalisar dattawa – Omo-Agege

- Sanata Omo-Agege ya sha alwashn cewa sai sun tsige Sarakidaga kujerar shi

- Yace da shi da sauran sanatocn APC zasu fatattaki shugaban majalisar dattawa daga majaisa

- Omo-Agege ya kuma jadadda cewa bazasu bari a tsige Buhari ba indai suna majalisa

Sanata mai wakiltan yankin Delta ta tsakiya, Ovie Omo-Agege, ya sha alwashin cewa shi da sauran sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), zasu tabbatar da cewar an dakatar da shugaban majalisar dattawa kuma sanata mai wakiltan Kwara ta tsakiya, Dr BuklaSaraki daa kujerarsa sannan su fatattake shi daga majalisar dattawa.

Sanata Omo-Agege ya kuma zargi Saraki da shirya makirci don tsige Shugaba Muhammadu Buhari inda ya kara da cewa indai har shi da sauran sanatocin APC na majalisar dattawa, baza’a yi nasara ba a duk wani yunkuri na tsigeBuhari.

Zamu tsige Saraki a matsayn shugaba, sannan mu fatattake shi daga majalisar dattawa – Omo-Agege

Zamu tsige Saraki a matsayn shugaba, sannan mu fatattake shi daga majalisar dattawa – Omo-Agege
Source: Depositphotos

Ya bayyana hakan a Sapele, jihar Delta lokacin day a ai ziyarar zanawa da shugabanni, dattawa da kuma shugabannin kananan hukumomi na APC a yankin Delta na tsakiya a kokarin shin a sake neman goyon bayansu a zabe mai zuwa.

A wai lamari na daban, mun ji cewa yan takara a karkashin jam’iyyar APC na ci gaba da nuna dari-dari da shuwagabannin jam’iyyar, biyo bayan tsadar kudin tikitin tsayawa takara da jam’iyyar ta sanar.

Rahotannin da Legit.ng ta tattara a Abuja, a ranar asabar, na nuni da cewa yan takara a jam’iyyar, da suka nuna sha’awar tsayawa takara a matakin gwamna, majalisun dokoki na kasa da ma shugaban kasa, na bayyana damuwarsu bisa tsadar da tikitin yayi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Dalilin da yasa nake son kujerar Dogara – Dan majalisa

Rahotanni sun bayyana cewa yan takarar sun bukaci da a rage kudaden da aka sanya. A baya bayan nan ne dai kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta APC, ya fitar da kudin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa akan Naira Miliyan 55, wanda ya haura Naira Miliyan 12 da jam’iyyar PDP ta sanyawa nata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel