Lema ta kara yagewa: Tsohon gwamanan PDP ya fita daga jam’iyyar

Lema ta kara yagewa: Tsohon gwamanan PDP ya fita daga jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Donald Duke, ya fita daga jam’iyyar PDP tare da bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamna Duke ya mulki jihar Kuros Riba na tsawon shekaru 8 a karkashin PDP kuma an dade ana tsammanin zai tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Duke ya bayyana ficewarsa daga PDP ne a yau, Talata, a shelkwatar jam’iyyar SDP inda sakataren jam’iyyar, Shehu Gabam, da sakataren yada labaran jam’iyyar, Alfa Mohammed, da sauran su suka tarbe shi.

Ya bayyana cewar ya fita daga jam’iyyarsa ta PDP wacce ya shafe kusan shekaru 20 a cikinta saboda yanzu ta rasa ma’ana da alkibla.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel