Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu garkuwa Mutane 3 a jihar Kano

Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu garkuwa Mutane 3 a jihar Kano

Da sanadin shafin jaridar Daily Nigerian mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta cafke wasu miyagun mutane uku da suka yi garkuwa da wani kankanin yaro dan shekara hudu a cikin tantagwaryar birnin jihar Kano dake Arewacin Najeriya.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Magaji Musa Majiya, shine ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin jihar a ranar Litinin din da ta gabata.

Majiya ya bayyana cewa, an cafke wannan miyagu a ranar 31 ga watan Agusta bayan da wani Muhammad Mustapha na unguwar Goron Dutse, mahaifin wannan yaro ya yi korafi akan dan sa, Al-amin Mustapha da suka nema suka rasa.

Binciken ya auku ne yayin da masu garkuwa da mutanen suka kirayi mahaifin yaron ta hanyar wayar tarho da lambar waya ta 08069777966, inda suka bayyana bukatar su ta neman fansar zunzurutun kudi na N100, 000.

Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu garkuwa Mutane 3 a jihar Kano

Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu garkuwa Mutane 3 a jihar Kano
Source: Facebook

Jami'an 'yan sandan sun bazama cikin gudanar da bincike da sanadin umarnin kwamishinan 'yan sanda na jihar, Rabi'u Yusuf, inda ba tare da daukar wani lokaci mai tsayi ba suka cika aikin da rataya a wuyan su.

KARANTA KUMA: Matasa sun raunata 'Yan sanda 2 tare da rushe Motar su ta sintiri a jihar Filato

Matasan da dukkanin su ba su wuci shekaru 24 a duniya ba da suka hadar da; Ibrahim Idris, Khalid Abdulrahman da kuma Ahmad Ibrahim Usman, sun shiga hannu inda karamin cikin su ya amsa laifin kulla wannan mummunan lamari da a yanzu suke da na sani baki daya.

A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan lamari inda daga bisani za a gurfanar da matasan gaban kuliya kamar yadda kakakin 'yan sandan ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel