Gyaran jadawalin zabe: PDP ta bukaci majalisa ta saka takalmin karfe ta take Buhari

Gyaran jadawalin zabe: PDP ta bukaci majalisa ta saka takalmin karfe ta take Buhari

- Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin cewa shugaba Buhari baya son a gudanar da sahihiyar zabe a 2019

- PDP ta yi kira ga majalisar tarayya tayi amfani da karfin ikon domin yin garambawul ga dokar zaben

- PDP tayi ikirarin cewa gyarar dokan zaben ya dara dalilan da shugaba Buhari ya bayar muhimmanci

Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga majalisar tarayya tayi amfani da karfin iko a kan batun yiwa dokan zabe na 2010 garambawul bayan shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa a yiwa dokar garambawul.

Cijewar Buhari kan dokar zabe: PDP ta kallubalanci Majalisa ta tursasa ta Buhari

Cijewar Buhari kan dokar zabe: PDP ta kallubalanci Majalisa ta tursasa ta Buhari
Source: Twitter

A sanarwan da Sakataren yada labaran jam'iyyar, Mr. Kola Ologbondiyan ya fitar a jiya Litinin, jam'iyyar ta ce ba tayi mamakin kin saka hannu kan kudirin dokar da shugaba Buhari ya yi ba domin shugaban kasa bashi da niyyar gudanar da sahihiyar zabe.

DUBA WANNAN: Barayin gwamnati sun fara birne kudade a makabartu da gidajen karkashin kasa - Gwamnan PDP

Mr. Kola Ologbondiyan ya ce dukkan 'yan Najeriya sun gani karara cewa dukkan dalilan da shugaba Buhari ya bayar na kin amincewa da yiwa dokar zaben garambawul dalilai ne marasa tushe.

Kalamansa: "Dukkan dalilan da shugaba Buhari na bayar na kin amincewa da yiwa dokar zabe garambawul ba su kai muhimmanci da ke tattare da yiwa dokar garambawul ba saboda gudanar da sahihiyar zabe a 2019.

"Hakan yasa, jam'iyyar PDP ke kira ga majalisar tarayya da tayi amfani da karfin ikon ta domin ganin cewa an gudanar da sahihiyar zabe da 'yan da 'yan Najeriya za su amince dashi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel