Yawan barazanar da APC take yi ba zai bata nasara a jihar Kwara ba - PDP

Yawan barazanar da APC take yi ba zai bata nasara a jihar Kwara ba - PDP

- Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kwara, ta ce babu barazanar da PDP za tayi da zai bata nasara akan PDP a jihar

- A cewar sakataren kudi na jam'iyyar, Chief Moses Ibiyemi, jam'iyyar ta samu karfi da hadin kai tun bayan da Saraki ya koma cikinta

- A baya dai shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya ce jam'iyyar zata yi nasara akan PDP tare da kwato jihar daga hannun Saraki a zaben 2019

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara, a ranar litinin ta jaddada cewar babu wata barazana daga jam'iyyar APC mai mulki da za tayi, har ya bata nasara akan PDP a jihar, idan aka zo babban zaben 2019.

Domin tabbatar da hakan, jam'iyyar ta PDP ta ce irin tsarin da shugaban majalisar dattijai, Dr. Bukola Saraki ya dora jam'iyyar a jihar, ya sa ta zamo mai cike da kuzari da hadin kai, wanda zai iya bata damar lallasa APC idan lokacin zabe ya zo.

A baya bayan nan Legit.ng ta ruwaito maku cewa, Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, a yayin da ya ke zantawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Abuja, ya buga kirji da cewar jam'iyyar zata samu nasara akan PDP tare da kwato jihar Kwara daga hannun Saraki a zaben 2019 da ke gabatowa.

Yawan barazanar da APC take yi ba zai bata nasara a jihar Kwara ba - PDP

Yawan barazanar da APC take yi ba zai bata nasara a jihar Kwara ba - PDP
Source: Twitter

KARANTA WANNAN: APC ta bayyana dalilin da ya sa ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Ilorin, a jiya litinin, Sakataren kudi na jam'iyyar PDP na jihar, Chief Moses Ibiyemi, ya ce: "A yanzu PDP ta zama daya, biyo bayan sauya shekar da Saraki yayi daga APC zuwa jam'iyyar, haka zalika, ta kara karfi bayan da ya gana da tsoffin mambobin jam'iyyar."

Ibiyemi, wanda ya gabatar da taron tare da shugaban jam'iyyar shiyyar Kwara ta kudu, Chief Ebun Afolayan da mataimakin shugaban jam'iyyar na jihar, Alhaji Mohammed Sani, ya ce: "A yanzu muna cike da hadin kai a jihar, babu sauran wariya a wasu wurare da hakan ta faru a baya, kuma zamu yi aiki kafa da kafada don ci gaban jihar."

Ya ce Saraki na aiki hannu-da-hannu da mambobin jam'iyyar da ya taras, "kuma mun dai daita tafiyar ofisoshin jam'iyyarmu da ke a fadin jihar don magance matsalolin da ka iya tasowa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel