Ba zan sake takara ba, bayan wannan karon - Makarfi

Ba zan sake takara ba, bayan wannan karon - Makarfi

- Tsohon shiguban riko na PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya ce ba zai sake fitowa takarar zabe ba muddin bai samu tikiti a PDP ba

- Makarfi ya yanke wannan shawarar ne saboda ya ce shekaru sun fara zuwa masa saboda haka ya kamata ya bawa yara fili

- Sai dai ya ce hakan baya nuffin ya dena siyasa domin zai cigaba da bayar da gudunmawarsa a jam'iyyar ta PDP

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya ce ba zai fice daga jam'iyyar PDP idan bai samu tikitin tara ba sai dai murabus daga takarar neman wata kujerar a kasar.

Ba zan kara takara idan ban samu tikiti ba - Daya daga cikin dan takaran shugban kasa a PDP

Ba zan kara takara idan ban samu tikiti ba - Daya daga cikin dan takaran shugban kasa a PDP
Source: Facebook

Sanata Makarfi ya yi wannan bayanin ne a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Kaduna inda ya ce shekaru sun fara zuwa masa saboda haka idan har bai yi nasarar samun tikitin ba a yanzu zai koma gefe guda ne ya rika bayar da gudunmawarsa amma ba zaiyi takara ba.

DUBA WANNAN: Barayin gwamnati sun fara birne kudade a makabartu da gidajen karkashin kasa - Gwamnan PDP

Kamar yadda wasu daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa a PDP kamar, Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso su kayi alkawari, Makarfi shima ya ce babu dalilin da zai sa ya fice daga jam'iyyar PDP ko da bai samu tikitin takarar zaben ba.

Da yake tsokaci kan batun sauya sheka da mutane da dama su kayi zuwa jam'iyyar PDP, Makarfi ya ce dama ya yi hasashen hakan zai faru saboda irin yadda jam'iyyar APC ke mayar da wasu saniyar ware.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC. Sauya shekarsa ba zai rasa nasaba da rushe shugabanin jam'iyyar na jihar da uwar jam'iyya tayi cikin kwana-kwanan nan duk da cewa kotu ta bayar da umurnin kada a aikata hakan.

DUBA WANNAN: Barayin gwamnati sun fara birne kudade a makabartu da gidajen karkashin kasa - Gwamnan PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel