Kwankwaso ya gano matsalar da yasa shugabanin baya suka gaza canja Najeriya

Kwankwaso ya gano matsalar da yasa shugabanin baya suka gaza canja Najeriya

- Sanata Kwankwaso ya ce mafi yawancin masu mulki a Najeriya basu da isashen ilimi da kwarewar aiki

- Kwankwaso ya ce babban matsalan Najeriya shine almubazaranci da kudi wajen bayar da kwangila

- Kwankwao ya ce Najeriya na bukatar shugaba da zai yi adalci ba tare da nuna banbanci kabila ko addini ba

Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da ilimi da kwarewa da zai iya jan ragamar mulkin Najeriya inda ya ce da yawa cikin shugabanin da muke dasu a yanzu basu da wayewar da zasu iya magance matsalolin kasar.

Kwankwaso ya gano matsalar da yasa shugabanin baya suka gaza canja Najeriya

Kwankwaso ya gano matsalar da yasa shugabanin baya suka gaza canja Najeriya
Source: Twitter

Kwankwaso ya fadi wannan maganar ne a jiya yayin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia a fadan gwamnatin jihar da ke Umuahia.

DUBA WANNAN: Barayin gwamnati sun fara birne kudade a makabartu da gidajen karkashin kasa - Gwamnan PDP

Kwankwaso ya kuma ce ya fice daga jam'iyyar PDP ne kafon zaben 2015 saboda yana tunatin jam'iyyar ta lalace amma daga baya ya gano cewa PDP ta dara APC sau goma.

Ya ce babban kalubalen da ake fuskanta a Najeriya wajen gudanar da ayyukan cigaba shine barnar kudade, inda ya kara da cewa akwai bukatar a sake duba yadda ake bayar da kwangila musamman a ma'aikataun gwamnati.

Sanatan mai wakiltan Kano ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ke da ilimi da kwarewa ta yadda zai iya fahimtar bukatun jama'an da ke dukkan sassan Najeriya.

"Najeriya na bukatar shugaban da zai rungumi kowa ba tare da nuna banbancin kabila ko addini ba.

"Shugaba da zai mayar da hankali wajen ganin an yiwa kowa adalci. Idan muka samu irin wannan shugaban a karagar mulki, ina kyautata zaton abubuwa zasu tafi yadda ya kamata," inji Kwankwaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel