Matasa sun raunata 'Yan sanda 2 tare da rushe Motar su ta sintiri a jihar Filato

Matasa sun raunata 'Yan sanda 2 tare da rushe Motar su ta sintiri a jihar Filato

Shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, matasan garin Lopandet na gundumar Du dake karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, sun kai hari kan hukumar 'yan sanda inda suka raunta biyu a yayin da suke bakin aiki a yankin.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Terna Tyopev, shine ya bayar da shaidar hakan ga 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai a yau Talata dangane da aukuwar lamarin a ranar Litinin din da ta gabata.

DSP Tyopev yake cewa, baya ga lahani da Matasan suka yiwa jami'an biyu, sun kuma lalata daya daga cikin motocin su na sintiri a yayin da suke bakin aiki a yankunan.

Kamafanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a daren ranar Lahadin da ta gabata ne wasu 'yan ta'adda da ake zargin makiyaya ne suka kai hari kan al'ummar wannan yanki inda suka salwantar da rayukan mutane 11 tare da jikkatar da dama.

Matasa sun raunata 'Yan sanda 2 tare da ƙona Motar su ta sintiri a jihar Filato

Matasa sun raunata 'Yan sanda 2 tare da ƙona Motar su ta sintiri a jihar Filato
Source: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da jami'an tsaro ke kai komo domin tabbatar da kiyaye doka a yankin, wasu fusatattun matasa suka nemi daukar fansa a kan hukumar 'yan sanda bisa zargn su kan zuba idanu dangane da wannan cin kashi na ɗauki ɗai ɗai da mahara ke yiwa al'umma a jihar.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'Yan ta'adda 31 a yankunan Arewa

Fushin matasan ya sauka ne akan jami'an 'yan sanda biyu da suka hadar da; sufeto James Gomos da kuma Sajen Mu'azu Adamu, inda a halin yanzu ke ci gaba da samun kulawa a asibitin jami'ai dake birnin Jos kamar yadda kakakin 'yan sandan ya bayyana.

Kazalika ya kuma gargadi matasan akan sake aukuwar wannan lamari a nan gaba, inda ya shawarce akan cewa hukumar ba ta nufin su da wata kiyayya face zaman lafiya irin abokanan zama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel