2019: Yan takaran PDP a Kogi sun hana a ba Melaye da sauransu tikitin tazarce

2019: Yan takaran PDP a Kogi sun hana a ba Melaye da sauransu tikitin tazarce

Yan takaran kujerun siyasa a zaben 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party have na Kogi sun nuna adawa akan shirin bayar da tikitin tazarce ga mambobin majalisun dokokin kasar.

Yan takaran da suka yi zanga-zanga a hedkwatar jam’iyyar dake Abuja a ranar, Litinin, 3 ga watan Satumba sunce a ba dukkanin yan takara damar da zasu ja daga.

Sunce zaben fidda gwani mai sahihanci ne kawai zasu amince mawa a fadin jihohin.

2019: Yan takaran PDP a Kogi sun hana a ba Melaye da sauransu tikitin tazarce

2019: Yan takaran PDP a Kogi sun hana a ba Melaye da sauransu tikitin tazarce
Source: Depositphotos

Masu zanga-zanga da suka jero baitukan wakoki kala-kala don nuna fushin su, sunce ba yan majalisa tikitin tazarce kamar irinsu Sanata Dino Melaye da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a kwanan nan zai zamo sabama dokar zabe da kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

A wani lamari makamacin wannan, Legit.ng ta samu labarin cewa w ata daya bayan sauya shekan Sanatan Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga All Progressives Congress (APC), rikici ya kunno kai cikin sashen jam’iyyar PDP a jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Cikin hotuna: Yan jam'iyyar PDP a jihar Kano sunyi zanga-zanga kan rikicin cikin gida

Wannan rikici ya fara ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta kasa ta sauke dukkan shugabannin jam’iyyar a jihar da kuma nada sabbin wadanda za su jagoranci mambobin jam’iyyar.

Rikici ya barke ne musamman tsakanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu manyan jigogin jam’iyyar PDP a jihar wadanda suka kunsho tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, Ambasada Aminu Wali, Sanata Bello Hayatu Gwarzo da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel