Rawar da Osinbajo ta taka wajen dawowan Shekarau APC

Rawar da Osinbajo ta taka wajen dawowan Shekarau APC

- Labarai sun fara bayyana kan dalilin da yasa Shekarau ya koma APC

- An jingina komawarsa APC da alkawuran Minista da mukamai

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zai alanta sauya shekarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Kano.

Jaridar Daily Nigerian ta samu labarin cewa Shekarau ya kasance cikin tattaunawa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tun lokacin da aka fara sauye-sauyen sheka daga jam’iyyun siyasa.

KU KARANTA: Rudani ya mamaye Maiduguri sakamakon fashewar bama bamai da harbin bindigogi

Majiya na cikin gida ya nuna cewa jam’iyyar APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujeran Minista idan ya dawo APC.

“Ka san Osinbajo tsohon lauyan Shekarau ne. Ka tuna Shekarau ya bashi dukkan karan kotu masu muhimmanci na gwamnatin jihar Kano da kuma wanda ya shafesa.”

“Osinbajo ya samu nasara kan wata mujallar da ta wallafa asusun bankin kasashen wajen da ake zargi Shekarau ke da su. Kana Osinbajo ya yi cinikayyar a madadin gwamnatin jihar Kano kan rikicinta kamfanin Pfizer.”

“Daga cikin alkawuran a dade da yi masa shine kujeran minister da wasu mukamai ga mabiyansa. Abinda ya hanashi komawa a lokacin shine karar da EFCC ta shigar da shi.”

“Amma ina tabbatar maka da cewa Shekarau zai koma APC yau. An gama dukkan shirye-shirye”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel