Rayuka 14 sun salwanta yayin da Makiyaya suka kai hari jihar Filato

Rayuka 14 sun salwanta yayin da Makiyaya suka kai hari jihar Filato

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wasu abin al'ajabi ya sake aukuwa a daren ranar Lahadin da ta gabata yayin da wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan fulani ne suka kai wani mummunan hari jihar Filato.

Harin ya auku ne a kananan hukumomin Jos ta Kudu da Bassa dake jihar ta Filato inda ya salwantar da rayukan kimanin rayukan mutane 14 kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sai dai ko shakka ba bu wannan hari ya auku ne a yayin da gwamnan jihar, Simon Lalong, ke cikin tawaragar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta halartar taron hadin kan kasashen Afirka da China a birnin Sin da za a gudanar a ranar 3 da 4 ga watan Satumba.

Rayuka 14 sun salwanta yayin da Makiyaya suka kai hari jihar Filato

Rayuka 14 sun salwanta yayin da Makiyaya suka kai hari jihar Filato
Source: Depositphotos

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan hari ya auku ne bayan kwana guda da korafin shugaban wata kungiya mai kare hakkin dan Adam, Mark Lipdo, da ya bayyana cewa makiyaya na kulle-kulle zartar da hare-hare cikin wasu kauyuka a fadin jihar.

KARANTA KUMA: Gwamnoni 5 na ƙulle-ƙullen warware shawarar Buhari ta zaben fidda gwani

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, daya daga cikin hare-haren ya auku ne a auku ne a kauyen Rati daura da garin Dogo Nahawa, inda makiyaya haye bisa baburan suka bude wuta ta harsasheb bindiga kan mai uwa da wabi da rayukan mutane 12 suka salwanta nan take.

Kakakin 'yan sanda na jihar Matthias Tyopev ya bayyana cewa, rayukan mutane 11 sun salwanta a yayin da mutane takwas suka raunata a yayin bayar da tabbacin sa dangane da aukuwar harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel