A matsayina na likita, zan iya bada tabbacin cewa Buhari ya fi kashi 80 na yan Nigeria koshin lafiya - Ngige

A matsayina na likita, zan iya bada tabbacin cewa Buhari ya fi kashi 80 na yan Nigeria koshin lafiya - Ngige

- Dr. Chris Ngige wanda ministan kwadago ne ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi kashi 80 na yan Nigeria koshin lafiya

- Ya ce yan Nigeria su zamo masu godiya ga Allah da ya basu Buhari a matsayin shugabansu la'akari da cewa shekaru da kwarewa ke samar da shugaba nagari

- Ngige ya ce gwamnatin tarayya zata sanar da sabon albashi mafi karanci a karshen watan Satumba

Kamar yadda Daily Independent ta ruwaito, Ministan kwadago Dr. Chris Ngige ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na da cikakkar lafiya da kuma kuzarin gudanar da shugabanci sabanin yadda wasu bata garin siyasa ke cewa shugaban kasar ya tsufa da yin shugabanci.

Dr. Chris ya yi nuni da cewa a lokacin da kasar Maleshiya ta shiga cikin rudanin siyasa da karywar tattalin arziki, Dr. Mahathir bin Mohammad, dan shekaru 90 ne ya zo ya ceci kasar bayan da ya zama Firan Minista.

"Shi Buhari da kuke gani ya fi kashi 80 na 'yan Nigeria koshin lafiya.

"Ni likita ne, a hukumance zan iya tabbatar da cewa yafi dukkanin wadanda ke korafi akan lafiyar sa isasshiyar lafiyar da zai mulki kasar nan. Ya zauna tsawon awanni takwas a taron majalisar zartaswa, ya yin da wasun mu zaka gansu suna zuwa shan iska ko cin abinci. Amma shi yana a zauna, ba ya cin komai illa Ruwa da ya ke sha har aka kammala"

KARANTA WANNAN: Nayi nadamar gudunmawar miliyoyin da na bawa APC a 2014 – Ekweremadu

A matsayina na likita, zan iya bada tabbacin cewa Buhari ya fi kashi 80 na yan Nigeria koshin lafiya - Ngige

A matsayina na likita, zan iya bada tabbacin cewa Buhari ya fi kashi 80 na yan Nigeria koshin lafiya - Ngige
Source: Twitter

Ngige ya ce ya zamarwa yan Nigeria wajibi su ci gaba da yiwa Allah godiya da ya basu Buhari a matsayin shugabansu, duba da cewa shekaru da kwarewa ce ke samar da shugaba nagari.

Dangane da batun da ke yawo na Buhari ya mayar da yankin Igbo saniyar ware, Ngige ya bukaci yan Nigeria da su kauracewa irin wadannan labaran kanzon kuregen.

A wani labarin:

Gwamnatin tarayya a ranar litinin, 13 ga watan Augusta, ta tabbatarwa yan Nigeria da kungiyoyin kwadago cewa sabon tsarin biyan albashi mafi karanci zai fara ne a karshen watan Satumba.

Ministan kwadago da daukar ma'aikata, Chris Ngige, ya ce gwamnatin tarayya zata sanar da sabon kudin albashi mafi karanci kafin karshen watan satumba, da nufin samar da kyakkyawan yanayin aiki ga yan Nigeria.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel