Kurunkus: Kwankwaso ya kwace jam'iyyar PDP a jihar Kano

Kurunkus: Kwankwaso ya kwace jam'iyyar PDP a jihar Kano

- Kwankwaso ya kwace jam'iyyar PDP a jihar Kano

- Uwar jam'iyya ta kasa ce rushe zababbun shugabannin jam'iyyar a jihar

- Ta kuma nada na hannun damar Kwankwaso a matsayin shugaban rikon kwarya

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu dake fitowa daga jihar Kano na nuni ne da cewa tsohon gwamnan jihar kuma Sanatan dake wakiltar shiyyar jihar ta tsakiya watau Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kwace shugabancin jam'iyyar.

Kurunkus: Kwankwaso ya kwace jam'iyyar PDP a jihar Kano

Kurunkus: Kwankwaso ya kwace jam'iyyar PDP a jihar Kano
Source: Twitter

KU KARANTA: Buhari yayi sabbin nade-nade guda 4

Wannan dai kamar yadda muka samu ya biya bayan zama shugaban kwamitin riko na jam'iyyar a mataki na jiha da tsohon Sakataren gwamnatin jihar kuma daya daga cikin makusanta kuma na hannun damar tsohon gwamna Kwankwaso, Alhaji Rabi'u Sulaiman Bichi yayi.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa jam'iyyar a mataki na kasa ta nada wani kwamitin mutane bakwai da zai ja ragamar jam'iyyar bayan rushe zababbun shugabannin jam'iyyar da tayi a jihar.

Sai dai kamar yadda muka samu, wannan matakin uwar jam'iyyar bai yi wa 'yan jam'iyyar a jihar dadi ba musamman ma daga bangaren tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau da suke ganin hakan tamkar keta masu haddi ne.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar adawa a jihar Kano ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi fatali tare da kin amincewa da matsayar da uwar jam'iyyar ta kasa ta dauka na sauke dukkan shugabannin zartarwar jam'iyyar daga Abuja.

Daya daga cikin jogogin jam'iyyar a jihar Kano mai suna Sarki Labaran da kuma ke zaman daya daga cikin na hannun daman tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ne ya sanar wa da wasu magoya bayan jam'iyyar da suka taru a hedikwatar jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel