Rudani ya mamaye Maiduguri sakamakon fashewar bama bamai da harbin bindigogi

Rudani ya mamaye Maiduguri sakamakon fashewar bama bamai da harbin bindigogi

- Rahotanni sun bayyana cewa an ji karar fashewar bama bamai da harbin bindigogi a Maiduguri, jihar Borno

- An ji karar fashewar bam din ne a kusa da madatsar ruwa ta Alau, nesa kadan da wajen garin

- Madatsar ruwa ta Alau, na biyawa akalla kashi 70 na mutanen yankin bukatunsu na yau da kullum

Rahotannin da ke zuwa mana a safiyar nan daga wata majiya mai tushe, na nuni da cewa an ji sautin fashewar bama bamai tare da harbin bindigogi, da ake kyautata zaton cewa mayakan Boko Haram ne suka kai hari a kusa da madatsar ruwa ta Alau da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Konduga.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa rundunar soji da ta hango wasu gungun yan ta'adda da ke haye a saman babura, a yankin na madatsar ruwa ta Alau, ta budewa yan ta'addan wuta da bindigogi masu sarrafa kansu gami da babbar bindiga mai fashewa kamar bam.

KARANTA WANNAN: Nayi nadamar gudunmawar miliyoyin da na bawa APC a 2014 – Ekweremadu

Madatsar ruwa ta Alau, wanda shine kusan hanya daya ta samar da ruwa ga sama da kaso 70 na al'ummar yankin, na ci gaba da fuskantar hare hare tun daga watan baya, sai dai gwamnatin jihar Borno na musanya wannan rahoton.

Har zuwa yanzu ba'a tantance ko akwai asarar rayuka ko jikkata a wannan sabon harin da yan ta'addan suka kai ba.

A wani labarin:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar lahadi, 2 ga watan Satumba, a birnin Beijing, kasar Sin, ya yin da ya ke zayyanawa yan Nigeria mazauna kasar Sin irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, ya ce zuwa yanzu babu wani yanki da ke karkashin mayakan Boko Haram a Nigeria.

Shugaban kasar ya alakanta wannan nasara da dumbin mayakan da aka tura sassa daban-daban na yankunan da mayakan Boko Haram suka mamaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel