Sanata Shehu Sani ya nemi Afrika ta cigaba da alaka da China

Sanata Shehu Sani ya nemi Afrika ta cigaba da alaka da China

Fitaccen Sanatan Jam’iyyar APC mai mulki Kwmared Shehu Sani yayi bayani a shafin sa na sadarwa na Tuwita inda ya nemi mutanen Yankin Afrika su cigaba da alaka da Kasar Sin watau China.

Sanata Shehu Sani ya nemi Afrika ta cigaba da alaka da China

Shehu Sani yayi kira Najeriya ta gujewa bashin China
Source: Twitter

Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya nemi Afrika ta karfafa alakar ta da China musamman a bangaren tattalin arziki. A cewar Sanatan, Kasar ta China babbar kawa ce ta Afrika. Sai dai kuma Sanatan ya nemi Najeriya ta bi a hankali da kasar.

Kwamared Shehu Sani ya nemi Najeriya da ma Afrika su guji maida kan su wuraren da Kasar China za ta rika kawo kaya marasa inganci su na jibgewa. Bayan nan kuma dai Sanatan ya nemi Najeriya ta bi a hankali da tsarin bashin China.

KU KARANTA: Zaben Osun zai tonawa Buhari a asiri inji Bukola Saraki

Har wa yau babban ‘Dan Majalisar na Jihar Kaduna ya bayyana cewa akwai bukatar China ta kara dagewa wajen ganin an daina nunawa bakaken fata na Afrika wariyar launin fata. Ana kukan cewa ana tsangwamar bakaken mutane a Kasar Sin.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai Sanatan ya nuna cewa Jam’iyyun da ake da su a Najeriya sun fara yin yawa. Sanatan a cikin ba’a yace takardar kada kuri’a za tayi tsawo tamkar zaren teloli a zabe mai zuwa na 2015 da za ayi nan gaba kadan.

Yanzu haka Shugaba Buhari yana Kasar China inda zai yi kusan mako guda.Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki Iyalin sa da Gwamnonin Jam’iyyar APC da dama da kuma Ministocin sa 9 da wasu Sanatoci 4 Tawagar sa zuwa Kasar ta China.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel