Sai-da-dan-gari: Wasu na zagaye da Buhari ne ke cutar sa - Inji wani jigo a APC

Sai-da-dan-gari: Wasu na zagaye da Buhari ne ke cutar sa - Inji wani jigo a APC

- Wasu na zagaye da Buhari ne ke cutar sa inji wani jigo a APC

- Yace shi shugaba Buhari mutumen kirki ne

- Ya bayar da misali da ministan matasa da wasanni

Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Delta dake ke kudu maso kudancin Najeriya Cif Ayiri Emami ya yi ikirarin cewa dayawa daga cikin wadanda ke zagaye da Shugaba Buhari sune ke dagula masa lissafi.

Sai-da-dan-gari: Wasu na zagaye da Buhari ne ke cutar sa - Inji wani jigo a APC

Sai-da-dan-gari: Wasu na zagaye da Buhari ne ke cutar sa - Inji wani jigo a APC
Source: UGC

KU KARANTA: Ana shirya makarkashiyar maida Lawal Daura aikin sa

Cif Ayiri yace musamman ma ministocin gwamnatin Shugaba Buhari kwata-kwata basu don suka cigaban sa kuma a lokutta da dama sukan zamo tamkar 'yan hana ruwa gudu a sha'anin tafiyar da gwamnatin ta sa.

Legit.ng ta samu cewa Cif Ayiri ya fadi hakan ne a lokacin dake zantawa da wakilin majiyar mu inda har ma ya bayar da misalin cikin ministocin Shugaba Buhari na wasanni da matasa watau Barista Solomon Dalung inda yace yana yakar gwamnatin ne ma a kai kai ce.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari kawo yanzu a iya cewa ya cika daya daga cikin alkawurran da ya daukar wa 'yan Najeriya a lokacin yakin neman zaben sa a shekarar 2015 bayan da ya farfado da kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya wata Air Peace.

Mun samu daga majiyar mu dai cewa yanzu kamfanin sufurin na Air Peace ya soma gudanar da zirga-zirgar dare daga garin Legas zuwa wasu kasashen nahiyar Afrika irin su Accra, Banjul da kuma Dakar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel