Jirgin Air Peace: Shugaba Buhari ya cika alkawarin sa ga 'yan Najeriya

Jirgin Air Peace: Shugaba Buhari ya cika alkawarin sa ga 'yan Najeriya

- Shugaba Buhari ya cika wani alkawarin sa ga 'yan Najeriya

- Kamfanin jiragen sufuri na Najeriya mai suna Air Peace ya soma aiki

- Yana daya daga cikin alkawurran da Shugaba Buhari ya dauka a 2015

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari kawo yanzu a iya cewa ya cika daya daga cikin alkawurran da ya daukar wa 'yan Najeriya a lokacin yakin neman zaben sa a shekarar 2015 bayan da ya farfado da kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya wata Air Peace.

Jirgin Air Peace: Shugaba Buhari ya cika alkawarin sa ga 'yan Najeriya

Jirgin Air Peace: Shugaba Buhari ya cika alkawarin sa ga 'yan Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani dan APC ya fadi abun da 'yan APC basu son ji

Mun samu daga majiyar mu dai cewa yanzu kamfanin sufurin na Air Peace ya soma gudanar da zirga-zirgar dare daga garin Legas zuwa wasu kasashen nahiyar Afrika irin su Accra, Banjul da kuma Dakar.

Legit.ng ta samu cewa shugaban dake kuma da ayyukan yau da kullum na kamfanin jiragen Mista Oluwatoyin Olajide ne ya bayyana hakan inda kuma yace sun fara da kasashen ne domin saukakawa 'yan Najeriya sufuri zuwa kasashen.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa lokacin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari, farfado da kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya yana daya daga cikin alkawurran da shugaban kasar yayi.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Delta dake a yankin kudu maso kudancin kasar nan sun tabbatar da sace wani babban malamin addinin kirista ajihar mai suna Rabaran Fada Christopher Ogaga a garin Oviri-Okpe dake a karamar hukumar Okpe.

Kamar dai yadda muka samu, Kwamishinan 'yan sandan jihar Alhaji Muhammad Mustafa shine ya sanar wa da manema labarai hakan a garin Warri, daya daga cikin manyan garuruwan dake a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel