Wasu Magoya bayan Buhari sun maidawa wani mutumi kudin da ya kashe wajen ganin APC tayi nasara a 2015

Wasu Magoya bayan Buhari sun maidawa wani mutumi kudin da ya kashe wajen ganin APC tayi nasara a 2015

Mun samu labari cewa wasu Magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun maidawa wani Bawan Allah kudin sa da ya kashe wajen yakin neman zaben Buhari da Osinbajo a 2015.

Wasu Magoya bayan Buhari sun maidawa wani mutumi kudin da ya kashe wajen ganin APC tayi nasara a 2015

Mohammad Baba ya nemi a maida masa kudin da ya kashe kan APC a baya
Source: Twitter

Muhammad Abdullahi Baba ya fito yana kuka inda yace ina ma ace a maida masa kudin sa da ya kashe wajen yi wa Buhari da Jam’iyyar APC kamfe a baya. Allah ya nufa kuma ya dace inda ya samu wani ya biya masa bukatar sa.

Daga cikin wannan bayani na Muhammad Abdullahi Baba a shafin sadarwa na zamani na Tuwita, sai wani Bawan Allah mai suna Ahmad Arkindhele ya tuntube sa domin ya maida masa kudin da yace ya kashewa jirgin yakin Buhari.

KU KARANTA: An ba hammata iska wajen wani taron Jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya

Wasu Magoya bayan Buhari sun maidawa wani mutumi kudin da ya kashe wajen ganin APC tayi nasara a 2015

An maidawa wanda ya taba ba Buhari gudumuwa kudin sa
Source: Twitter

Abdullahi Baba yayi ikirarin cewa ya sa kudin sa har N2000 a asusun kamfen din Jam’iyyar APC lokacin da Janar Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo su ke neman takarar shugabancin kasar nan shekaru kimanin 3 da su ka wuce.

Ahmad Arkindhele ya aikawa wannan Bawan Allah da yayi da-na-sanin wannan aiki na sa kudin sa N2000 ta bankin sa na Diamond kuma ya tabbatar da cewa kudin sun shigo. Masoyan Shugaban kasa Buhari sun yabawa wannan mutumi.

Wani Bawan Allah shi kuma ya koka da duk wannan abin da ya faru yana mai yin tir da lamarin inda yace ina ma ace shi ma za a biya sa kudin da ya kashe wuri-na-gugar-wuri har N50000 domin ganin Muhammadu Buhari yayi nasara a zaben 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel