An gargadi Shugaban APC Oshimhole ya fasa shirin da ya dauko ko ayi maganin sa

An gargadi Shugaban APC Oshimhole ya fasa shirin da ya dauko ko ayi maganin sa

Rikicin da ake fama da shi na cikin gida a Jam’iyyar APC na cigaba da yin gaba. Yanzu dai har ta kai Majalisar dokokin Jihar ta fara nuna Shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole da ‘dan yatsa.

An gargadi Shugaban APC Oshimhole ya fasa shirin da ya dauko ko ayi maganin sa

Ana zargin Shugaban Jam'iyyar APC Oshimhole da shiryawa Gwamnoni gadar-zare
Source: Depositphotos

Kamar yadda labari ke zuwa mana, Kakakin Majalisar Jihar Adamawa watau Kabiru Mijinýawa ya gargadi Adams Oshiomhole game da shirin da yake yi na cusa mutum miliyan 2 a matsayin ‘Ya ‘yan Jam’iyyar ta APC mai mulki.

Kabiru Mijinýawa ya fadawa Shugaban na APC cewa idan bai bi sannu ba. Za su yi maganin sa. Kakakin Majalisar yayi wannan jawabi ne a Garin Yola inda yace APC na kokarin shiryawa Gwamnan Jibirilla Bindow manakisa.

KU KARANTA: Tazarcen Buhari zai kawo karshen iskancin su Saraki

APC na yunkurin amfani da ‘Yar tinke inda kowane ‘Dan Jam’iyya zai yi zabe wajen fitar da ‘Yan takara na zaben 2019. Mijinýawa yana ganin wannan shiri zai kawowa Gwamnan na Adamawa Jibirilla Bindow cikas a zabe mai zuwa.

Shugaban Majalisar dokokin Jihar Adamawa yace an kawo sunayen ‘Yan APC na bogi har fiye da mutum miliyan 2 wanda za ayi amfani da su wajen zaben fitar da gwani. Mijinyawa yace yana da hujjojin da zai nunawa Shugaba Buhari.

Jiya kun ji labari cewa an ba hammata iska wajen wani taron ‘Yan taware na Jam’iyyar APC a Jihar ta Adamawa. Rigima ta barke ne tsakanin Gwamnan Adamawa da wasu manyan APC game da shirin fitar da ‘Yan takara na zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel