Nayi nadamar gudunmawar miliyoyin da na bawa APC a 2014 – Ekweremadu

Nayi nadamar gudunmawar miliyoyin da na bawa APC a 2014 – Ekweremadu

Ike Ekweremadu, mataimakin shugaban majalisar dattijai, ya ce ya taimakawa APC da gudunmawar miliyan N5m a shekarar 2014 lokacin da ake kokarin kafa jam’iyyar.

Da yake ganawa da jama’ar mazabarsa a jihar Enugu, Ekweremadu, ya ce ya taimakawa jam’iyyar APC ne saboda Dakta Chris Ngige, ministan kwadago, ya nemi taimakonsa.

Jam’iyyu uku ne suka dunkule wuri guda domin kafa jam’iyyar APC a shekarar 2014.

Ekweremadu ya bayyana cewar babu abinda zai saka jam’iyyar PDP faduwa zaben shekarar 2015 da a ce tsohon shugaban kasa Jonathan ya kasance mai son rai.

Nayi nadamar gudunmawar miliyoyin da na bawa APC a 2014 – Ekweremadu

Ike Ekweremadu
Source: Depositphotos

Zan fada maku wani abu da zai matukar girgiza ku. A shekarar 2014, lokacin da aka kirkiri APC, Sanata Chris Ngige ya kira ni tare da bukatar taimako na wajen samun nasarar yiwa jama’a rijista a jam’iyyar. Lokacin ina matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai a jam’iyyar PDP amma duk da haka na bayar da gudunmawar miliyan N5m ga jam’iyyar,” a cewar Ekweremadu.

DUBA WANNAN: Zamu tika Buhari da kasa - Mata 6 dake takarar shugaban kasa

Sannan ya cigaba da cewa, “gabanin zaben shekarar 2015, wata mata ta zo ta same ni tare da shaida min zata yi takarar neman kujerata ta sanata a jam’iyyar APGA kuma tana neman taimakona. Na ce mata ba matsala, zan biya kudin sayen fom dinki na takara saboda ina son ganin kowacce jam’iyya ta gabatar dad an takara. Ta fadi zaben amma duk da haka na taimaka mata wajen samun mukamin siyasa.”

Kokarin jin ta bakin Chris Ngige domin tabbatar da maganar Ekweremadu bai samu ba saboda wayarsa a kashe take lokacin da jaridar The cable ta kira shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel