Sanata David Mark ya mika ragamar PDP babin Benue ga Gwamna Ortom

Sanata David Mark ya mika ragamar PDP babin Benue ga Gwamna Ortom

An mika ragamar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) babin jihar Benue ga Gwamnan jihar Samuel Ortom a ranar Litinin, 3 ga watan Satumba.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark ne ya mika ragamar mulkin a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Makurdi, babban birnin jihar.

Mark ya bayyana cewa taron masu ruwa da tsakin ya kasance farko da jam’iyyar ta gudanar tun bayan dawowa Otom jam’iyyar.

Sanata David Mark ya mika ragamar PDP babin Benue ga Gwamna Ortom

Sanata David Mark ya mika ragamar PDP babin Benue ga Gwamna Ortom
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa manyanmutanen dasuka dawo PDP ya nuna cewa jam’iyyar zata iya lashe kowani zabe a kasar.

KU KANTAN KUMA: 2019: Yawan yan takara ba zai tarwatsa PDP ba - Shekarau 2019: Yawan yan takara ba zai tarwatsa PDP ba - Shekarau

Ya kara da cewa daga tsoffi har sabbin mambobi na da yanci iri guda a ja’iyya, inda yace don haka ya zama dole ayi garambawul a shugabaninjam’iyyar domin ayi tafiyar tare da wadada suka saua sheka zuwa jam’iyyar a baya-bayan nan.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Daid Mark ya bayyana cewa a gobe Talata, 4 ga watan Agusta zai sayi takardan takarar zaben kujeran shugaban kasa a 2019 karkashin jam’iyyar PDP.

An tattaro cewa Sanata David Mark wanda aka fi sani da :Okpokpowulu K’Idoma” zai tsaya takara da sauran masu neman kujeran shugaban kasar guda goma sha biyu.

Haka zalika Ortom yayialkawarin yin aiki tare da kowa domin gudanar da jagoranci mai inganci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel